Nawa ne albashin shugaban ƙasar Amurka?

Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon
Nawa ne albashin shugaban ƙasar Amurka?

Mutane kan yi tunanin cewa shugaban ƙasar Amurka na samun maƙudan kuɗaɗe a matsayin albashi da alawus-alawus.

Babu kuskure a wannan tunanin saboda shugaban Amurka jagora ne na ɗaya daga cikin ƙasashe mafiya girma, kuma mafiya ƙarfin iko a duniya.

Amma fa ba haka abin yake ba kwatakwata.

Dalili shi ne an tsara duk shugaban da ke mulkin Amurka zai zama ma'aikacin gwamnati ne, akan biya su albashi ne da harajin da sauran 'yan ƙasa ke biya.

Shugaba Joe Biden da ke mulki a yanzu na karɓar dala 400,000 a shekara.

Amma kuma ba shi ne kuɗin da Donald Trump sabon shugaba mai zuwa zai karɓa ba