An sanya wa'adin karshe na kasashen da ke son daukar nauyin gasar Nations Cup 2025

Senegal ce ta ci gasar da aka yi a 2021, kuma a farkon shekarar nan ne aka bayyana mane a matsayin gwarzon nahiyar

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Senegal ce ta ci gasar da aka yi a 2021, kuma a farkon shekarar nan ne aka bayyana mane a matsayin gwarzon nahiyar

Hukumar kwallon kafa ta CAF ta sanya ranar 11 ga watan Nuwamba a matsayin wa'adin karshe ga kasashen da ke da muradin karbar bakuncin gasar Afrika ta 2025.

Ana neman samun sabuwar kasar da za ta karbi bakunci bayan Guinea ta gaza cika tsammanin da ake da shi a kanta na samar da wuraren wasa da kayan aiki don gasar.

CAF na sa ran samun bukata ta karshe daga kasashe da suka hada da takardunsu da kuma biranen da ake so a yi wasanni cikinsu, a kai su hedikwatarta da ke Cairo nan da ranar 16 ga watan Disamba.

Wakilina CAF da za su duba wuraren za su fara aikin dubawar ne daga ranar 5 ga watan Janairu zuwa 25, a laluben da take yi na neam wadda za ta maye gurbin Guinea. Za a gabatar da bayanan da kwamitin kolin CAF su 24 suka samu, wanda kuma a ranar 10 ga watan Fabirairu za a sanar da kasar da ta samu nasara ko kasashen da za su hada gwiwa domin karbar bakuncin wasannin.

Wani babban jami'in CAF ya shaida wa BBC cewa hukumarsuna kokarin kaucewa bai wa "duk wata kasa da bata da filayen wasa da kuma karamci da za a nunawa sauran sassan duniya".

Kamaru ce ta dauki bakuncin 2021, kuma a farkon shekarar nan aka sauya Ivory Coast da za karbi bakuncin gasar a 22023 amma aka mayar da shi 2024 saboda wasu dalilai irin na yanayi.

Ana tsammanin Morocc za ta nema Tuni wasu kasashe suka nuna sha'awarsu ta daukar nauyin gasar kashi ta 35, amma har yanzu ba su nuna sha'awarsu a hukumance ba.

Morocco wadda ta karbi bakuncin gasar Afrika Ta Mata a watan Yuli, tana da niyyar daukar bakuncin gasar ta maza ta 2025, kamar yadda wani jami'i a hukumar kwallon kafa ta Morocco ya tsegunta.

Najeriya da ta nuna bukatar daukar gasar ta hadin gwiwa da Benin itama ta yi tsit tun bayan da Amaju Pinnick ya sauka daga shugaban hukumar ta NFF.

Bukatar Algeriya da Afrika Ta Kudu da kuma Senegal suma an ta yada jita-jitan za su iya daukar wannan gasar.

Hoton wani filin wasa a Ivory Coast wanda za a yi wasa a cikinsa a 2023

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Hoton wani filin wasa a Ivory Coast wanda za a yi wasa a cikinsa a 2023