Makarantar allon da almajiranta ba sa yin bara a Kano

Bayanan bidiyo, Makarantar allon da almajiranta ba sa yin bara a Kano
Makarantar allon da almajiranta ba sa yin bara a Kano

Danna hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Madinatul Ahbab, makarantar allo ce a unguwar Fagge da ke Kano wadda aka kafa a shekarar 1954 da manufar koyar da karatun Qur'ani.

Makarantar ta banbanta da sauran makarantun allo ta hanyar kange almajiranta daga yin bara kasancewar mahaifan yaran ne ke tura musu abinci.

Wani abun da ya kara banbanta makarantar da sauran makarantun na allo shi ne yadda ake koyar da ilimin zamani.