Yadda ƴan Najeriya suka yi zanga-zangar matsin rayuwa a ranar farko

Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyo
Yadda ƴan Najeriya suka yi zanga-zangar matsin rayuwa a ranar farko

Ƴan Najeriya na yin zanga-zanga kan matsin rayuwa sanadiyyar tashin gwauron-zabi na farashin kayan masarufi, wanda ba a taɓa gani ba a shekarun baya-bayan nan.

Hukumomi sun roƙi masu zanga-zangar da su janye, amma abin ya ci tura. Alhamis, ɗaya ga watan Agusta ne ranar farko ta zanga-zangar wadda aka tsara yin ta a tsawon kwana 10.