Amorim na tunanin murabus daga Man Utd, Tottenham na zawarcin Guehi

Ruben Amorim

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 1

Waɗansu majiyoyi daga cikin Old Trafford na cewa mahukuntan Machester United na tunanin kocin ƙungiyar ɗan ƙasar Portugal Ruben Amorim, mai shekaru 40, zai iya yin murabus tun kafin a kai ga koran sa. (iPaper)

Tottenham na cikin jerin ƙungiyoyin da ke neman ɗan wasan baya na Crystal Palace da Ingila Marc Guehi mai shekara 25. (CaughtOffside)

Ɗan wasan tsakiya na Real Madrid ɗan ƙasar Uruguay Federico Valverde, mai shekara 27, ya kasance ɗaya daga cikin ƴan wasan da Manchester United za ta yi zawarci a bazara mai zuwa. (Fichajes)

Kocin Tottenham Thomas Frank na sha'awar ɗaukar ɗan wasan bayan Jamhuriyar Ireland Nathan Collins, mai shekara 24, daga Brentford. (TBRFootball)

Ɗan wasan tsakiya na Tottenham da Uruguay Rodrigo Bentancur, mai shekara 27, ya gab da ƙulla sabuwar yarjejeniya da kulob ɗin na arewacin Landan (Football.London)

Ɗan wasan tsakiya na Barcelona Dro Fernandez, mai shekara 17, ba shi da niyyar sauraron duk wani tayin da za a yi masa daga ƙasashen waje, duk da cewa Arsenal da Chelsea da Manchester City na zawarcin sa. (TBRFootball)

Fulham na shirin zawarcin ɗan wasan Middlesbrough ɗan ƙasar Ingila Hayden Hackney, mai shekara 23. (Football League World)