Da galan ɗaya na fara sana'ar baƙin mai - Mai kamfanin Ammasco

Bayanan bidiyo, Tun ina sakandire na fara sana’ar baƙin mai - Mai Ammasco
Da galan ɗaya na fara sana'ar baƙin mai - Mai kamfanin Ammasco

Mai kamfanin baƙin mai ko man inji na Ammasco ya shawarci matasan arewacin Najeriya su tashi tsaye su rungumi sana'o'i da kuma kafa kamfanoni, inda ya nuna cewa da rarrafe yaro kan tashi.

Alhaji Mustapha Ado ya ce dubban ma'aikata ne ke aiki yanzu a kamfaninsa, harkar da ya fara tun daga sayar da galan na man inji lokacin da yake karatun sakandire.

Daga baya ya zo yana sayar da diro-diro na man kafin ya fara sauke mota, har yanzu ya mallaki kamfani ya kuma zama shugaban masu kamfanonin baƙin mai a Najeriyar.

Ya ce a yanzu yana da burin kafa har matatar man fetur nan gaba, kuma bai ga dalilin da ya sa matasa su ma ba za su tashi su kafa harkokin kasuwancinsu ba.

Ma'aikata

Ɗaukar bidiyo da tacewa: Umar Ladu