Hira da sabon shugaban ƙungiyar gwamnonin Arewacin Najeriya Muhammad Inuwa Yahaya
Hira da sabon shugaban ƙungiyar gwamnonin Arewacin Najeriya Muhammad Inuwa Yahaya
Sabon shugaban ƙungiyar gwamnonin Arewacin Najeriya ya ce za a iya magance dimbin matsalolin da ke addabar yankin ne kawai idan al’ummarsa ta hadu kan manufa daya kuma ta yi da gaske wajen magance su.
A cikin wata hira da sashen Hausa na BBC, Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya na jihar Gombe ya ce zai yi aiki tukuru domin tabbatar da yankin na arewa wanda ake yi wa kallon kurar baya, ya kamo sauran bangarorin kasar ta fuskoki daban-daban na ci gaba rayuwa.



