Mun samu matsaya a Arewa maso Yamma kan 'yan fashin daji - Uba Sani
Mun samu matsaya a Arewa maso Yamma kan 'yan fashin daji - Uba Sani
Gwamna Uba Sani na Kaduna ya yi bayani a kan ƙoƙarin da gwamnatinsa take yi wajen yaƙi da matsalolin tsaro da suka addabi jiharsa, da ke arewa maso yammacin Najeriya.
Ɓangaren da ya fi fama da rikicin 'yan fashin daji a ƙasar. Gwamnan a wannan hira ta musamman da Sashen Hausa na BBC ya ce ya tuntuɓi takwarorinsa gwamnoni da jihohinsu ke fama da hare-haren 'yan fashin daji kuma sun cimma matsaya kan yadda za su tunkare su.




