Ba mu da isassun kayan aikin tunƙarar ƴan bindiga - Babban hafsan tsaron Najeriya

Bayanan bidiyo, Latsa sama don kallon bidiyon
Ba mu da isassun kayan aikin tunƙarar ƴan bindiga - Babban hafsan tsaron Najeriya

Babban hafsan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa ya ce sojojin ƙasar ba su da isassun kayan aikin tunƙarar ƴan bindiga da ke ci gaba da addabar mutane a sassan ƙasar.

Janar Christopher Musa ya bayyana haka ne a wani taron manema labarai a Abuja.

Ya ce ba su samun isassun kayan yaƙi, inda ya ce ko da sun je kasuwa ba sa iya samun kayakin.

"Manyan ƙasashe su ke da waɗannan kayaki, amma suna hana mu," in ji shi.

Ya ƙara da cewa akwai hannu wasu mutane a batun garkuwa da mutane shiyasa matsalar ta-ki-ci-ta-ki-cinyewa.

Ya ce ya kamata al'umma su tashi don ba da tasu gudummawa a yaƙi da ƴan bindiga, inda ya bukace su da su riƙa bayar da rahoton duk wani abu da ba su yarda da shi ba.

Har ila yau, babban hafsan tsaron Najeriyar ya ce kwamitin da suka kafa don gudanar da bincike kan harin Tudun Biri ya kammala bincikensa, inda ya ce kafin karshen wata za a bayyana abin da binciken ya gano.

A ɗaya gefen, ya ce albashin da sojoji ke karɓa bai taka kara ya ƙarya ba.

"Albashin sojoji bai kai 50,000 ba, ko ni idan na je wurin yaƙi abinci da ake ciyar da ni naira 1,200 ne," in ji shi Christopher Musa.

Sai dai ya ce shugaban ƙasa ya bayar da umarnin a sake duba batun albashin, kuma yana da tabbacin cewa za a ƙara shi.