Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Champions League: Ko Barca za ta iya doke PSG?
Za a ci gaba da wasa na uku-uku a cikin rukuni a Champions League ranar Talata, inda za a yi karawa tara a filaye da dama a fadin nahiyar Turai.
Daga cikin wasannin da za a buga akwai wadanda za su jan hanjalin yan kallo da ya hada da Paris St Germain da na Barcelona.
Ita dai Barcelona tana kan ganiya a kakar nan, wadda ta lashe dukkan wasa tara a La Liga da maki 27 da kuma nasara biyu a Champions League.
Ita kuwa Parst St German tana ta biyu a kan teburin Ligue 1 da maki 14, bayan cin wasa hudu da canjaras biyu aka doke karawa daya, sannan ta yi nasara a wasa biyu a Champions League a kakar nan.
Haka kuma wasan Liverpool da Villarreal zai ja hankalin yan kallo, yayin da Manchester City za ta buga wasa na 150 a Champions League.
City za ta karbi bakuncin AEK Athens a Etihad, koda yake wannan shi ne karon farko da kungiyoyin za su fuskanci juna a gasar ta Champions League.
Wasannin ranar Talata 20 ga watan Oktoba
- Fenerbahçe vs Slavia Praha
- Sabah vs Borussia Dortmund
- Roma vs Slovan Bratislava
- Porto vs PSV Eindhoven
- Liverpool vs Villarreal
- Manchester City vs AEK Athens
- Paris Saint-Germain vs Barcelona
- Napoli vs Bodø/Glimt
- Stuttgart vs Atlético de Madrid
Mohammed Abdu ya hada rahoto kan wasu daga cikin wasannin da za su fi jan hankali.
Paris Saint-German vs Barcelona
Ferran Torres ya bar Barcelona ya koma Paris St Germain kwanaki 12 kafin a raba jadawalin wasannin bana a Champions League – ɗan wasan Sifaniya ya ci ƙwallo 65 a wasa 207 da ya buga wa ƙungiyar Camp Nou. Dro Fernández ma ya sauya sheƙa daga Barcelona zuwa babban birnin Faransa a watan Janairu, bayan ya buga wasa biyar kacal.
Ousmane Dembélé ya yi kaka shida a Barcelona daga 2017 zuwa 2023), inda ya zura ƙwallo 40 a wasa 185 tare da lashe kofunan La Liga uku kafin ya koma PSG.
Ya zura ƙwallo a kowanne daga cikin wasanni shida a baya-bayan nan a Champions League, inda ya yi kan-kan-kan da tarihin Kylian Mbappé da ya yi wannan bajintar a 2021/22.
Kocin PSG na yanzu, Luis Enrique ya ja ragamar Barcelona daga 2014 zuwa 2017, kuma shi ne ya sa kungiyar ta lashe manyan kofi uku har da Champions League a kakar 2014/15.
PSG ba ta yi rashin nasara ba a wasanni 12 na baya-bayan nan a Champions League ba, ta yi nasara takwas da canjaras hudu, tun bayan shan kashi da ci 2-1 a hannun Sporting CP a watan Janairun 2026.
Kungiyar na fatan kara cin wasa daya nan gaba domin yin kafada da tarihin wasa 13 a jere ba tare da rashin nasara da ta kafa tsakanin kakar 2012/13 zuwa 2013/14).
Kocin Barcelona, Hansi Flick, ya doke PSG da ci 1-0 tare da Bayern Munich a wasan ƙarshe a Champions League a 2020, amma ya sha kashi a hannunsu a wasan daf da na kusa da na ƙarshe a kakar 2020/21, sannan ya sake yin rashin nasara da ci 2-1 tare da Barcelona a matakin lik a kakar bara.
Ƙungiyar Barcelona ta yi wasa 17 aka zura mata kwallo a baya-bayan nan a Champions League, wanda shi ne mafi tsawon irin wannan tarihin a gasar. Haka kuma an zura mata ƙwallo da fara wasanni sau takwas daga cikin 11 na baya-bayan nan da ta buga a Champions League.
A wannan rana a shekarar 2020, Pedri ya ci ƙwallo a wasansa na farko a Champions League yayin da suka lallasa Ferencváros da ci 5-1 a gida – kuma har yanzu ita ce ƙwallonsa kaɗai a gasar.
Andreas Christensen ya ci ƙwallonsa ta farko a gasar a wannan rana a shekarar 2021, lokacin da yake tare da Chelsea a nasarar da suka yi da ci 4-0 kan Malmö.
Lamine Yamal ya taka rawa kai tsaye da sa hannu a cin ƙwallaye biyar a wasa biyu da Barcelona ta buga a matakin lig a kakar bana, wanda ya ci ƙwallo ɗaya da ya kuma bayar da hudu aka zura a raga.
Wasannin da aka buga tsakanin Paris St Germain da Barcelona:
2025/2026
European Cup Laraba 1 ga watan Oktoba 2025
- Barcelona 1 - 2 PSG
2023/2024
Champions League Talata 16 ga watan Afirilu 2024
- Barcelona 1 - 4 PSG
Champions League Laraba 10 ga watan Afirilu 2024
- PSG 2 - 3 Barcelona
2020/2021
Champions League Laraba 10 ga watan Maris 2021
- PSG 1 - 1 Barcelona
Champions League Talata 16 ga watan Fabrairu 2021
- Barcelona 1 - 4 PSG
2016/2017
Champions League Laraba 8 ga watan Maris 2017
- Barcelona 6 - 1 PSG
Champions League Talata 14 ga watan Fabrairu 2017
- PSG 4 - 0 Barcelona
2014/2015
Champions League Talata 21 ga watan Afirilu 2015
- Barcelona 2 - 0 PSG
Champions League Laraba 15 ga watan Afirilu 2015
- PSG 1 - 3 Barcelona
Champions League Laraba 10 ga watan Disamba 2014
- Barcelona 3 - 1 PSG
Champions League Talata 30 ga watan Satumba 2014
- PSG 3 - 2 Barcelona
2012/2013
Champions League Laraba 10 ga watan Afirilu 2013
- Barcelona 1 - 1 PSG
Champions League Talata 2 ga watan Afirilu 2013
- PSG 2 - 2 Barcelona
1996/1997
Euro Cup Winners Cup Laraba 14 ga watan Mayu 1997
- Barcelona 1 - 0 PSG
1994/1995
Champions League Laraba 15 ga watan Maris 1995
- PSG 2 - 1 Barcelona
Champions League Laraba 1 ga watan Maris 1995
- Barcelona 1 - 1 PSG
Wasan Liverpool da Villarreal
Dominik Szoboszlai na Liverpool da Péter Gulácsi na Villarreal sun taka leda tare a Leipzig tsakanin 2021 zuwa 2023, kuma dukkansu suna buga wa ƙasar Hungary tamaula. Gulácsi ya kuma kasance a Liverpool tsakanin 2008 zuwa 2013, amma bai taɓa buga wa babbar ƙungiyar wasa ba. Szoboszlai (45) ne ya fi kowanne ɗan wasan Hungary yawan buga wasa a wannan gasar, yayin da Gulácsi (42) ke biye da shi a matsayi na biyu.
Alisson Becker da Virgil van Dijk sun buga kowane minti a wasa biyu lokacin da Liverpool ta doke Villarreal da jimillar ƙwallaye 5-2 a wasan kusa da na ƙarshe a kakar 2021/22. Juan Foyth ma ya yi hakan a ɓangaren kungiyar Sifaniya.
Liverpool ta yi nasara a wasa biyar a baya-bayan nan da ta buga da ƙungiyoyin Sifaniya a gasar UEFA, ciki har da huɗun da ta yi da ta buga a gida.
Liverpool ta yi nasara a wasa 15 daga cikin 16 na baya-bayan nan da ta buga a gida a matakin rukuni ko matakin lik a Champions League da rashin nasara daya.
Villarreal ba ta taɓa doke wata ƙungiyar Ingila ba a Champions League, wadda ta yi canjaras shida aka doke ta 10.
Nasarar da Villarreal ta samu a ranar wasa na biyu a rukuni a kan Napoli ta kawo ƙarshen jerin wasa 12 ba tare da samun nasara ba a Champions League, inda ta yi canjaras biyu aka doke ta 10.
An ci Villarreal ƙwallon farko a kowane daga wasa bakwai na baya-bayan nan da ta buga a waje a Champions League.
Manchester City za ta buga wasa na 150 a Champions League
Wasan City da AEK Athens a ranar Talata zai kasance na 150 da za ta buga a gasar Champions League/European Cup.
Sai dai wannan ne karon farko da ƙungiyoyin biyu za su kara da juna a tsakaninsu a babbar gasar ƙwallon ƙafa ta zakarun Turai.
Sai dai wannan tarihi da City za ta buga ya zo ne a kakar ta 15 a jere a babbar gasar Turai da take zuwa, wanda shi ne mafi tsawon lokaci da kowace ƙungiyar Ingila ke yi a halin yanzu.
Tun daga wannan lokaci taba lashe Champions League a kakar 2023 da yin ta biyu a 2021 da zuwa zagayen kwata fainal sau shida a tarihi.
Gaba ɗaya City ta yi nasara a wasa 83 daga cikin 149 da ta buga a gasar Champions League, inda ta ci ƙwallaye 313, sannan aka zura mana 180.
Kakar 2022/23 babu shakka ita ce mafi tarihi da ta samu a tarihin Champions League, inda ta doke irin su Bayern Munich da Real Madrid kafin ta yi nasara a kan Inter da ci 1-0 a wasa mai cike da kalubale a Istanbul ta kuma lashe kofin.
Bernardo Silva ne ya fi kowa wakiltar City a Champions League, inda ya sanya mata riga sau 86.
İlkay Gündoğan ne ke biye da shi da wasa 77, sai Ederson da 76, Fernandinho da 74, yayin da Kevin De Bruyne ya cika jerin biyar din farko da wasa 73.
Erling Haaland ne kan gaba a jerin masu yawan cin ƙwallaye a gasar Champions League, inda ya zura ƙwallo 38 a wasa 41.
Hasali ma, ya zarce Sergio Agüero, wanda ya ci ƙwallo 36 a wasa 64 bayan ƙwallonsa ta farko da ya ci a kan Paris Saint-Germain ranar Laraba.
Bayan Agüero, akwai Raheem Sterling da ya ci mata kwallo 24 a wasa 67 da Gabriel Jesus mai kwallo 20 a wasa 39 da Phil Foden da ya ci mata kwallo 20 a wasa 69 a matsayin waɗanda suka fi yawan cin ƙwallaye a gasar a City
Real Madrid ce ƙungiyar da City ta fi fuskanta, har sau 17.
Bayern Munich da Paris Saint-Germain ne ke biye da ta fafata da kowacce sau takwas, sai Borussia Dortmund da suka hadu karo bakwai.
Pep Guardiola ne kan gaba da ya ja ragamar wasa 105 daga cikin 149 da ta buga kawo yanzu, inda ya yi nasara 64 da rara ƙwallaye +124.
Manuel Pellegrini ya jagoranci ƙungiyar wasa 28 a tsawon shekara uku da ya yi a matsayin kocin City, inda ya yi nasara 13.
Roberto Mancini ya jagoranci wasanni 12, amma ya samu nasara uku kacal, yayin da Joe Mercer ya kasance kocin ƙungiyar a shekarar 1968.
Ziyarar da AEK Athens zuwa City, shi ne karo na uku da Enzo Maresca zai jagoranta, bayan ya yi nasara a kan Porto, sannan ya yi rashin nasara a Paris Saint-Germain a farkon kakar 2026/27.
Wasan Roma da Sloban Bratislava
2011/2012
Europa League Alhamis 25 ga watan Agusta 2011
- Roma 1 - 1 S. Bratislava
Europa League Alhamis 18 ga watan Agusta 2011
- S. Bratislava 1 - 0 Roma