Yadda tururuwar ƴan Rasha ta janyo tsadar haya a Dubai

.

Asalin hoton, ARETHA PRETORIUS

Bayanan hoto, Aretha da Chris da kuma 'yarsu Bella na shirin komawa wani ƙaramin gida, amma kuɗin hayarsa ya kai kashi 32

Watannin Fabrairu da Maris sun kasance masu wahala ga Aretha Pretorius.

Ita da mijinta sun shafe tsawon makonni suna yawo a Dubai don neman sabon gidan da za su koma.

Sun zauna a wani gida mai ɗaki uku da ke tsakiyar birnin tun cikin 2019.

Sai dai a shekara da ta gabata, mai gidan ya sanar wa iyalan cewa su tashi, ba zai ci gaba da ba su haya a kan kuɗi ƙalilan ba, idan nasu ya ƙare a watan Maris saboda yana shirin tarewa a gidan.

Sun fara neman wani gida ne a kusa da wurin, sai dai, sun kaɗu lokacin da suka ji cewa kuɗin haya a shekarar, ya tashi zuwa kashi 75 a kan $34,000 da suke biya a baya.

Sun faɗaɗa neman gida zuwa wasu unguwanni na Dubai, sai dai sun kasa samun daidai na kuɗinsu.

Daga baya, sun samu wani ƙaramin gida mai nisa daga tsakiyar birnin, kuma duk da haka, za su biya $45,000 - kashi 32 ƙari a kan kuɗin hayar da suke biya a baya.

''Mun shafe tsawon makonni muna ta neman gida. Sai dai ba mu da zaɓi illa mu amince da ɗan gidan da muka samu. A yanzu za mu zauna cikin ƙaramin gida, duk da yake muna biyan kuɗi da yawa," in ji Aretha.

Gidan zai kasance na biyar da Aretha da Chris suka zauna ciki a Dubai, tun bayan zuwansu daga Afirka ta Kudu a 2011. Kasuwar gidaje a Dubai ta yi ta sauyawa cikin gomman shekaru da suka gabata.

Sai dai Aretha ta ce ba su taɓa shan wahala wajen neman gida kamar wannan karon ba.

"Kuɗaɗen haya sun ƙaru a cikin shekara 10, amma ba a wahala wajen neman gida kamar yadda abin yake yanzu," in ji Aretha.

.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Kusan kashi 90 na al'ummar Dubai miliyan 10 sun kasance ƴan ƙasashen waje
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Kuɗin haya mafi ƙaranci a Dubai ya kai kashi 35 a bara, in ji cibiyar hada-hadar gidaje ta Betterhomes.

Ba mutanen da ke neman manyan gidajen haya ne kaɗai ke shan wahala ba. An samu ƙarin kuɗin haya a dukkan fannoni.

Tashin kuɗin haya, na ƙara jefa ƴan ƙasashen waje mazauna Dubai cikin wahala, musamman ganin su ne ƙashin bayan tattalin arziƙin katafaren birnin.

Kusan kashi 90 na al'ummar Dubai miliyan 10 ƴan ƙasashen waje ne.

Ƙaruwar kuɗin hayar ya tilasta wa mutane irinsu, Waquar Ansari barin Dubai zuwa birnin Sharjah mai makwabtaka, wurin da kuɗin ke haya ke da sauƙi.

Waquar da iyalansa suna zama ne a gida mai ɗaki ɗaya da ke kudancin Dubai, inda suke biyan $9,500 a shekara.

Lokacin da kuɗin hayarsa ya kusa ƙarewa a watan jiya, mai gidan ya so ya ƙara $3,000 a kan kuɗin hayar da yake biya.

Tun da farko, Ansari ya nemi sabon gida a wani wuri daban, amma kuɗin ya ƙaru da kashi 40.

"Ina da niyyar biyan ƙarin kashi 10 -15, sai dai na duba wasu unguwannin na Dubai, amma ban samu gida a farashin da nake so ba.

Zaɓi ɗaya ya rage min, shi ne na koma Sharjah," in ji Ansari.

.

Asalin hoton, BETTERHOMES

Bayanan hoto, Richard Waind na cibiyar hada-hadar gidaje ta Betterhomes ya ce yawan mutanen ke komawa Dubai ya fi yawan gidajen da birnin yake da su a yanzu

Babban Manajan cibiyar harkar gidaje ta Betterhomes, Richard Waind, wanda ke zaune a Dubai, ya ce mutanen da ke zuwa birnin, sun fi yawan gidajen da ake da su.

"Akwai mutane da yawa waɗanda ke zuwa Dubai idan aka kwatanta da gidajen da ake da su. Ana samun tsaiko wajen samun gida, abin da kuma ke janyo ƙara tsawwala kuɗin haya," in ji Waind.

A tsarin dokokin yaƙi da ƙarin kuɗin haya a Dubai - hauhawar farashi zuwa wani mataki - na bai wa masu gidaje damar su ma, su ƙara kuɗin haya ga mutanen da suka kama gidajensu da kashi 20.

Masu gidajen ba su da damar lorar ƴan haya, ba tare da wata ƙwaƙƙwarar hujja ba.

Sai dai masu gidajen haya da dama waɗanda ba su so a ambaci sunayensu, sun faɗa wa BBC cewa an ba su sanarwar su fice daga masu gidajen da suke ciki, waɗanda su ma suka ce suna son komawa gidajen da zama.

Amma waɗanda suka kama hayar, sun yi iƙirarin cewa hakan ba gaskiya ba ne, inda suka ce masu gidajen na son ba da hayar ne ga wasu mutane a kan babban farashi.

Sai dai ba kuɗin haya ne kaɗai ya tashi a Dubai ba - kuɗin sayen gidaje ma ya yi matuƙar tashi.

Kuɗin hayar ya ƙaru da kashi 35 a 2022, idan aka kwatanta da shekara ta 2020, lokacin ɓullar annobar korona, sa'ar da kuɗin ya ƙaru da sama da kashi 50, a cewar kamfanin harkar gidaje na Savills.

Kuɗin ƙasar Rasha ya kasance abin da ya janyo farashin haya ke ƙara tashi a Dubai, tun bayan soma yaƙin Ukraine a bara, in ji Katie Burnell, darakta a kamfanin harkokin gidaje na Savills da ke Dubai.

Dubai ta zamo wuri da hamshaƙan masu kuɗi da ƴan kasuwan Rasha ke zuwa don neman mafaka. Yawancin matasa ƴan asalin Rasha su ma sun koma birnin, inda suke neman wuraren aiki.

Kamfanoni da dama sun kwashe ma'aikatansu daga Rasha zuwa Dubai.

.

Asalin hoton, SAVILLS

Bayanan hoto, Kuɗin ƙasar Rasha ya kasance abin da ya janyo farashin haya ke ƙara tashi a Dubai, a cewar Katie Burnell ta kamfanin Savills

Ƴan Rasha sun kasance waɗanda suka fi zuba jari daga waje a harkar gidaje cikin birnin Dubai bara.

"Akwai takunkumai da dama a kan ƴan Rasha musaman game da wurin da za su zauna ko kuma su sayi kadara. Ba su da wannan matsala a Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa. A nan suna iya yin kasuwancinsu yadda suke so," in ji MS Burnell.

"Saboda wannan damar, ba sa damuwa da tsadar gida, kuma a shirye suke su biya haya kowanne farashi aka yanka musu."

An ƙiyasta cewa dubban mutane ne suka bar Rasha tun fara yaƙi da Ukraine, duk da yake, babu wani tabbataccen rahoto da ya bayyana ainihin yawan alƙaluman.

A cewar wani rahoton mujjalar Forbes, ƴan asalin Rasha 700,000 ne suka bar ƙasar tun bayan umarnin Shugaba Putin na taƙaita zirga-zirga da kuma kiran da ya yi na a shiga aikin soji cikin watan Satumban bara.

Sai dai fadar Kremlin ta musanta alƙaluman da mujalar ta fitar.

Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ba ta nuna goyon baya ba ko kuma amincewa da yaƙin Ukraine. Ba ta sanya wa Rasha takunkumi ba, kuma ba ta soki lamirin Rasaha kan mamayar Ukraine ba.

Ta ci gaba da bai wa ƴan Rashar da ba a saka wa takunkumi ba biza, sai dai Ƙasashen Yamma da dama sun ƙaƙaba wa Rashar takunkumi.

A watan da ya gabata, Babban Bankin Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ya bai wa bankin MTS mallakar Rasha lasisin fara aiki. Ƴan Rasha da dama na fuskantar wahalhalu wajen buɗe asusun banki da kuma aika kuɗi a Dubai saboda takunkuman Ƙasashen Yamma a kan bankunan Rasha da dama.

Tun ɓarkewar annobar korona, UAE ta bijiro da tsarin biza na dogon lokaci, inda hakan ya kawo ƙarshen buƙatar wanda zai ɗauki nauyin mutum - abin da ya taimaka wajen janyo hankalin ɗumbin masu zuba jari da ma'aikata da ƴan kasuwa zuwa ƙasar.

Yadda ƙasar ta kawar da annobar korona cikin hanzari, ya taka rawa matuƙa wajen ƙara janyo masu zuba jari daga ƙasashe da dama a faɗin duniya.

Dubai ta buɗe wuraren yawon buɗe, kuma ta cire takunkumin da ta sanya a 2020 saboda annobar korona, lokacin da yawancin ƙasashe a Turai ke cikin dokar kulle.

.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Kuɗin sayen gidaje a Dubai ya kai kusan $56.6bn a bara - wanda ya kai kashi 80 a 2021

Dubai ta ce an sayar da gidaje sama da 86,000 bara, inda alƙaluman suka ɗara wanda aka samu a 2009, wato 80,000.

An sayar da gidaje da kuɗinsu ya kai kusan $56.6bn a bara, inda aka samu kashi 80 fiye da a shekara ta 2021.

Richard Waind ya ce abubuwan da suka faru a duniya cikin shekara da ta wuce, ciki har da annobar korona da yaƙin Ukraine, sun ƙara tabbatar da matsayin Dubai na kasancewa mai arziƙi, da sanya kasuwar gidaje ta yi sama.

"Dubai na da tsaro yadda ya kamata da sauƙin yin kasuwanci, ga kwanciyar hankali. Wannan na cikin abubuwan da suka sanya mutane daga ƙasashe da dama ke hijira zuwa nan saboda damarmaki"

A bara, masu harkar gidaje sun sanar da shirin gina sabbin gidaje don daidaita ƙarin buƙatunsu da mutane ke yi.

Sai dai mista Waind na sa ran cewa tsadar haya zai ci gaba da kasancewa har tsawon aƙalla wata 18 - 24 kafin a kammala gina sabbin gidaje don rage yawan bukatu.

Akwai damuwar da ake nunawa cewa muddin kuɗin haya ya ci gaba da ƙaruwa, mutane za su kasa samun muhalli, abin da kuma da zai janyo da yawan mutane su fice daga Dubai zuwa wasu biranen na Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa.

"Eh, akwai yiwuwar hakan, abin da kuma ke da muhimmanci kuɗin haya ya fara sauka nan da wani ɗan lokaci ƙanƙani," in ji mista Waind.