Aston Villa na nazari kan Garnacho, Brighton na hari Diego Gomez

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Aston Villa na duba yiwuwar ficewa daga yarjejniyar ɗaukar Alejandro Garnacho daga Chelsea a matsayin ɗan wasan ta na din-din-din, idan har ba a sami ci gaba ba a ƙwazon ɗan wasan ba. (Football Insider)

Ɗan wasan Ingila Jadon Sancho, da kwantaraginsa ta ƙare, na son ganawa da manajan Getafe, kafin ya kai ga tsayar da matsayar sa kan komawa Sipaniya da taka leda zuwa ƙarshen kakar wasa. (Telegraph - subscription required)

Brighton ba zata siyar da Diego Gomez, a watan Janairu ba, duk da zawarcin ɗan wasan da Atletico Madrid da AC Milan ke yi. (Teamtalk)

Ɗan wasan Real Madrid da Jamus Antonio Rudiger, ya mayar da hankalinsa kan ci gaba da zamansa a Bernabeu maimakon alaƙanta shi da ake yi da Tottenham. (Bild - in German)

Masu ne man jagorancin Manchester United da za su iya maye gurbin Michael Carrick sun haƙiƙance cewar ƴan wasan ƙungiyar ne matsalar ƙungiyar sannan sun fiye surutu. (Telegraph - subscription required)

Liverpool na shirye-shireyen siyen ɗan wasan Barcelona Ronald Araujo da ke zaman ɗn wasan aro a ƙungiyar, kan euro miliyan 55, biyo bayan ƙwazon da ya nuna a wasannin da ƙasar sa ta uruguay ta buga. (Marca - in Spanish)

babau tabbas kan makomar ɗan wasan gaban Brazil Endrick a Real Madrid, inda ake hasashen cewar ɗan wasan na iya barin ƙungiyar na da watan Janairu a matsayin ɗan wasan aro zuwa AC Mila ko Roma, duk da cewar Jose Mourinho ya ce hakan ba mai yuwuwa ba ne. (Marca - in Spanish)

Dani Olmo ba shi da shirin barin Barcelona, duk da cewar ana alaƙanta shi da Bayern Munich.(Sky Sports Germany)

A shirye Atletico Madrid ta ke wajen ganin an sauya kwantaragin Jonathan David daga ɗan wasan aro a Juventus zuwa ta siyar da shi kan Euro miliyan 25, sai dai har yanzu basu cimma matsaya ba kan matakin. (Sky Sports Germany)