Kalli yadda tsohuwa mai shekara 96 ke ɗaga ƙarfen motsa jiki

Bayanan bidiyo, Kalli yadda tsohuwa mai shekara 96 ke ɗaga ƙarfen motsa jiki
Kalli yadda tsohuwa mai shekara 96 ke ɗaga ƙarfen motsa jiki

Matasa da dama kan ji ƙyashin motsa jiki hatta a cikin ɗakunansu, ballantana zuwa wani wuri.

Amma babu mamaki wannan dattijuwar mai shekara 96 a Vietnam za ta iya ƙarfafa muku gwiwar yin atasaye domin inganta lafiyar jikinku.

Tun bayan da ta fara zuwa ɗaga ƙarfe tare da taimakon jikanta, mutane da dama ke sha'awar zuwa ganinta da kuma ɗaukar hoto da ita.