Ku San Malamanku tare da Sheikh Ali Isa Fezzan

Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallo
Ku San Malamanku tare da Sheikh Ali Isa Fezzan

An haifi Sheikh Ali Isa Fezzan a unguwar Fezzan da ke birnin Maiduguri kimamin shekara 52 da ta gabata.

Ya fara karatu a makarantun allo kamar yadda aka saba a al'adance wajen karatun addinin Musulunci.

Daga mahafinsa ya kai shi makarantar Ma'at da ke birnin Maiduguri domin samun karatun ilimi.

Bayan nan ya zarce makarantar Higher Islamic da ke birnin Maiduguri a matsayin sakandire.

Daga nan ya zarce Jami'ar Maiduguri inda ya karanta fannin Ilimin addinin Musulunci inda ya kammala a 1997, sannan ya koma jami'a domin wani digirin a fannin Shari'a, inda yanzu haka yake digirinsa na biyu a fannin Shari'ar.

Ya fara koyarwa a sashen ilimi a ƙarƙashin gwamnatin jiha, kafin ya koma ƙarƙashin gwamnatin tarayya, inda yanzu haka yake a matsayin mataimakin darakta.

Ya yi karatu a wajen malaman da ya tasirantu da su kamar, Dakta Muhammad Salisu Baffa da Malam Muhammadu Na'inna.