Abin da kuke son sani kan katsewar lantarki a arewacin Najeriya

Bayanan bidiyo, Latsa hoton sama ku kalli bidiyo:
Abin da kuke son sani kan katsewar lantarki a arewacin Najeriya

Kwana 10 kenan zuwa yanzu tun bayan ɗaukewar lantarki a mafi yawan arewacin Najeriya.

Hukumomi sun yi zargin cewa 'yanbindiga ne su tunkuɗe layin wutar da ke kai wa arewa maso yamma, da arewa maso gabas, da wani ɓangare na arewa ta tsakiya wutar.

Sai dai har yanzu babu tabbas game da lokacin da za a kammala gyaran wutar, wadda hukumar TCN ta ce an fara a jihar Neja.