Yadda 'yan siyasar Indonesiya ke zuwa wajen bokaye da 'yan tsubbu
Yadda 'yan siyasar Indonesiya ke zuwa wajen bokaye da 'yan tsubbu
Indonesia ce ƙasar da ta fi kowace ƙasa yawan musulmai a duniya, to sai dai duk da haka bokaye da matsubbata na cin karensu babu babbaka a ƙasar.
A ranar 14 ga watan Fabrairun da muke ciki ne, fiye da al'ummar ƙasar miliyan 200 za su kaɗa ƙuri'unsu a zaɓen shugaba ƙasar da na 'yan majalisun dokokin ƙasar.



