Me ya sa ƙasashe ke rigegeniyar komawa duniyar wata?

Asalin hoton, NASA
- Marubuci, Angela Henshall
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
- Lokacin karatu: Minti 7
Tawagar farko da za ta nufi duniyar wata a cikin shekaru sama da 50 ana shirin tashi cikin makonni masu zuwa.
Tawagar Nasa Artemis II za ta iya tashi a kowane lokaci daga cikin watan Maris zuwa farkon Afrilu.
Amma hakan ya danganta da abubuwa da dama, ciki har da tabbatar da lafiyar kumbon da za a harba, da daidai inda watan ya ke da kuma yanayi.
Yayin da ƴan sama jannatin da za su shiga kumbon ba za su taka ƙafa a duniyar wata ba, NASA na fatan tafiyar ta kwanaki 10 na "slingshot" za ta ba da hanyar da za ta kai ga "zama mai ɗorewa a duniyar wata da kuma safarar Amurkawa zuwa duniyar Mars".
Amma ba wai Amurka kaɗai ke neman komawa duniyar wata ba.
Me yasa a halin yanzu ƙasashe ke gaggawar kai wa sararin samaniya kuma menene ke tattare da sabon tseren zuwa sararin samaniya?

Asalin hoton, NASA/Sam Lott
Mene ne maƙasudin tafiyar
Akasin sauran shirye-shiryen zuwa duniyar wata a shekarun 1960 zuwa 70, wannan tafiya ba aika mutane su je su dawo ba ne kaɗai, in ji Dokta Namrata Goswami, marubuciyar littafin 'Scramble for the Skies', ta shaida wa BBC.
Madadin haka, wani mataki ga Amurka a manufarta ta tabbatar da zama ta dindindin a duniyar wata da kuma haƙo ma'adanai masu mahimmanci, in ji ta.
Yana biye ne da shirin Artemis I,wani kumbo marar matuƙi da aka harba a shekarar c2022 wanda shi ne gwajin farko na sabon tsarin binciken sararin samaniya mai zurfi na NASA.
Daga cikin wasu ayyuka, ƴan sama jannatin da ke cikin Artemis II za su gudanar da aikin shirya jirgin Orion don sake ziyartar wata a nan gaba.

Asalin hoton, Getty Images
Me ya sa aka ɗauki tsawon lokaci kafin komawa?
Lokaci na ƙarshe da ɗan'adam ya taka ƙafa a duniyar wata shine shirin Apollo 17 na NASA a shekarar 1972 lokacin yaƙin cacar baka.
A wancan lokacin, Amurka ta riga ta lashe tseren na zuwa sararin samaniya, bayan da ta sanya ƴan sama jannati a duniyar wata a karon farko a shekarar 1969 - nasarar da Tarayyar Soviet ba ta taɓa samu ba.
Bayan cimma burinta, ba ta samu wani dalili na sake komawa duniyar wata ba, wanda aiki ne mai ɗan karen tsada, in ji Goswami.
Shirin Apollo daga 1961 zuwa 1972 ya ci zunzurutun kuɗi sama da dalar Amurka biliyan 25 - kwatankwacin dala biliyan 290 zuwa dala biliyan 320 a kuɗin yau.

Asalin hoton, Bettmann Archive/Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Amma duk da haka, tun daga wannan lokacin, an samu gagarumin ci gaba a fannin fasaha, kamar bunƙasa ayyukan rokoki da za a iya sake amfani da su da kamfanin SpaceX na Elon Musk da Blue Origin na Jeff Bezos suka yi ya taimaka wajen rage tsadar shirin, wanda ya haifar da bunƙasa fannin fara balaguro zuwa sararin samaniya da kuma ƙarin ƙasashe masu neman faɗaɗa bincikensu a sararin samaniya.
Fiye da ƙasashe 70 yanzu suna da nasu shirye-shiryen sararin samaniya na ƙasa.
Amma wataƙila babban abin da ya sa Amurka ta sabunta burin zuwa duniyar wata shin ne ƙasar China da ci gaba da samun nasararta a wannan fannin.
A shekarar 2019 ƙasar China ta zama ƙasa ta farko da ta sauka a gefen wata mai nisa inda ta yi amfani da kumbon bincikenta na Chang'e-4.
Goswami ta ce saukar jirgin "ta farkar" da Amurka, tana mai kwatanta hakan da ''zamanin Sputnik'' - tana nufin tauraron ɗan'adam na Soviet wanda shi ne na farko da aka harba a sararin samaniya a 1957.
Ta ƙara da cewa, "Sun yi la'akari da cewa, 'wow, China ba ta yin koyi da fasahar Rasha.'
Tun kafin ci gaban China, Donald Trump ya fito ƙarara ya ƙuduri aniyar mayar da ƴan sama jannati zuwa duniyar wata da binciken sararin samaniya a lokacin da ya rattaba hannu kan wata doka ta sararin samaniya a shekarar 2017 a lokacin mulkinsa na farko a matsayin shugaban Amurka.
A lokacin, ya ce dokar za ta "tabbatar da shirin Amurka a sararin samaniya ya sake kasancewa kan gaba kuma ya zanburar da ɗaukacin bil'adama.

Asalin hoton, ADEK BERRY/AFP via Getty Images
Mene ne muhimmanci komawa duniyar wata?
Yayin da China ke musanta cewa tana tseren zuwa sararin samaniya da Amurka, masana sun yi imanin cewa an riga an fara gudanar da wannan tseren na ganin ƙasa ta farko da za ta koma duniyar wata.
Yawancin manazarta sun yi imanin cewa ƙasashen farko da za su fara kasancewa a duniyar wata zama wadanda za su mamaye wuraren samar da albarkatu masu muhimmanci, kamar ɓangaren kudancin duniyar inda aka gano ruwa da ƙanƙara.
Ana iya amfani da wannan don samar da ruwan sha da iskar oxygen har ma da man roka.
Hakan zai rage buƙatar tsara shirye-shiryen sararin samaniya masu tsadar gaske daga doron ƙasa da kuma ƙara sa rai na manufa zuwa duniyar Mars a nan gaba, in ji masana.
Baya ga ruwa, an kuma gano wasu albarkatu a duniyar wata - ciki har da ƙarafa da ake amfani da su wajen gine-gine, irin su sanholo da titanium - da dai sauransu.
Wurin da ba kasafai ake samun isotope na helium ba, isotope helium-3 mai daraja sosai, inda ya kai dala miliyan 20 a kowace kilogiram wanda kuma a ƙarshe ana iya amfani da shi don samar da wutar lantarki da makamashin nukiliya.
Amma fitar da albarkatun kamar helium-3 yana da matuƙar wahala. Ƙalubalen da ake fuskanta sun haɗa da kayan aikin haƙar ma'adinai suna jure yanayin zafi daga 120°C (248F) a cikin hasken rana zuwa -170°C (-274F) da dare.
Aikin haƙar ma'adinai na helium-3 a nan gaba zai buƙaci zuba jari mai yawa da kuma hanyar sarrafa ƙasa mai yawa na wata.
"Domin a samu alfanun duk abin da ake buƙata, dole ne a iya fitar da shi, ku sayar da shi, ku sami riba daga gare shi ta hanyar da ta dace, da kuma darajar jarin da za ku je ku samo shi tun da farko," in ji Libby Jackson, shugaban ɓangaren sararin samaniya a gidan tarihi na Kimiyya a Burtaniya.
"Dole ne ku aiwatar da wani abu kamar metric ton na regolith na wata, ko ƙasa, don samun helium-3 ɗan kaɗan."

Asalin hoton, Bloomberg via Getty Images
Waye zai fara isa duniyar wata?
Ana kallon Amurka da China a matsayin manyan masu ƙarfin shirye-shiryen da suka shafi sararin samaniya.
Amurka na fatan isa duniyar wata da shrinta na Artemis III, inda sanya wa kanta wa'adin 2027.
Ita ma ƙasar China ta sanya wa kanta burin isa a shekarar 2030.
Sai dai ba su kaɗai ne ƙasashen da ke da burin isa duniyar watan ba.
Indiya, wadda ke samun ci gaba cikin sauri a fasahar sararin samaniyarta, na da burin sanya ƴan sama jannati a duniyar wata nan da shekara ta 2040.
A watan Agustan shekarar 2023, ta zama ƙasa ta huɗu a wancan lokacin - bayan Amurka, Rasha da China - da ta sauke kumbo a duniyar wata, kuma ta farko da ta fara bincike a ɓangaren kudancin watan.
Kuma duk da cewa ba ta taɓa amincewa da wannan burin a bainar jama'a ba, wani rahoto a shekarar 2023 ta kamfanin dillancin labaran ƙasar ta Tass ya ce Rasha na shirin aikewa da ƴan sama jannati zuwa duniyar wata a shekarar 2031 zuwa 2040.
To wa zai fara zuwa can?
Wasu masana sun yi imanin cewa a yanzu Beijing tana kan gaba, bayan da ta samu ci gaba cikin sauri a fannin fasaha da kuma ba ta samu koma baya kamar shirin Artemis ba.
Goswami ta ce sakamakon wannan sabuwar rige-rigen zuwa sararin samaniya "ya ma fi na farko muhimmanci".
A yanzu haka akwai ƙasashe sama da 70 "tare da cibiyoyi da hukumomin sararin samaniya masu sha'awar bunƙasa tattalin arziki da albarkatun wata," in ji ta.












