BBC ta gano kasadar da ƴan Najeriya ke yi wajen tafiya Turai ci-rani
BBC ta gano kasadar da ƴan Najeriya ke yi wajen tafiya Turai ci-rani
Duk shekara dubban ƴan ci-rani ne daga Najeriya ke fata tafiya Turai.
Shekara 20 da suka wuce, wani mai bayar da umarni a fina-finan kudancin Najeriya Ike Nnaebue, ya yi ƙoƙarin yin irin wannan bulaguron.
Da yake waiwaye kan abin da ya faru da shi a wancan lokacin, Ike ya ce ya haɗu da ƴan ci-rani da dama.
Ya ji dalilansu na barin gida da son yin tafiyar da kuma hadarin da ke gabansu.
Ya hadu da yan ci-ranin da suka samu karayar arziki da wadanda suka rasa tudun dafawa da ma wadanda suka fuskanci hare-haren wariyar launin fata.
Wasu kuma sun tsinci kansu a hannun masu safarar mutane.
Ga wadanda suka samu isa Moroko kuwa, sun cika da zumudin cewa dab suke da shiga Turai, amma kuma da yawansu hakan ma ya zame musu gagarumar matsala.



