Na'urar da za ta taimaka wa masu ciwon ƙashin baya yin tafiya

Bayanan bidiyo, Na'urar da za ta taimaka wa masu ciwon ƙashin baya yin tafiya
Na'urar da za ta taimaka wa masu ciwon ƙashin baya yin tafiya

Wani injiniya ɗan ƙasar Kanada Jonathan Tippett ya ƙera wani jikin ƙarfe mafi grima a tarihi.

Jikin ƙarfen mai suna “mech suit” – an yi shi ne don taimaka wa masu fama da lalurar ciwon ƙashin baya.

Sannan kuma zai taimaka wa mutane wajen ɗaga kaya masu matuƙar nauyi ba tare da sun ji a jikinsu ba.

Kundin abubuwan mamaki na duniya na Guinness ya ce na'urar mai ƙafa hudu ita ce mafi girma da aka taɓa samarwa a duniya da irin wannan manufar.