Zaɓen Ghana: Yadda mutane ke tururuwar komawa garuruwansu don kaɗa ƙuri'a

Bayanan bidiyo, Latsa hoton sama ku kalli bidiyo:
Zaɓen Ghana: Yadda mutane ke tururuwar komawa garuruwansu don kaɗa ƙuri'a

Dubban yan kasar Ghana na ci gaba da ficewa daga manyan birane zuwa garuruwansu na asali domin jefa ƙuri’unsu.

Sakamakon haka, ana samun karancin motocin sufuri da kuma cincirindon fasinjoji a tashoshin mota.

Wakilin BBC Haruna Shehu Tangza ya ziyarci tashar Ghana Station da ke Kumasi - birni na biyu mafi girma a kasar - na lura da yadda tashar ta cika da fasinjoji da kayayyaki da ke dakon motocin da za su dauke zuwa garuwansu.