An kashe wani babban kwamandan IS a Syria da Iraƙi

IS

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 1

Gwamnatin Iraqi ta ce jami'an leken asirinta sun kashe wani babban kwamandan kungiyar IS a Iraqi da Syria a wani farmaki da suka kai tare da dakarun Amurka.

Amurka ma ta tabbatar da kai farmakin da ya kai ga kashe kwamandan na IS Abdallah Makki Muslih al-Rifa, da ake kira Abu Khadija, inda Donald Trump ya ce dakarun Amurka ne suka yi farautarsa.

Firaministan Iraqi Mohammed Shia al-Sudani ne ya tabbatar da kashe kwamandan na IS, wanda firaministan ya kira hatsabibin ɗanta'adda a Iraqi da duniya bakidaya.

Amurka ta ce an kai harin ne da ya kai ga kashe kwamandan na IS a yammacin lardin Anbar ranar Alhamis.

Amurka kuma ta bayyana kwamandan na IS Abdallah Makki Muslih al-Rifa a matsayin daya daga cikin manyan masu fada a ji a kungiyar kuma wanda ke da alhakin bayar da umarni da tsare tsaren IS a duniya.

Ta ce bayan kai harin an samu Abu Khadija ne a mace tare da wasu mayakan IS, kuma dukkaninsu suna dauke da makamai da rigar ƙunar baƙin wake.

Gwamnatin Iraqi ta ce an tabbatar da shi ne bayan gudanar da gwaji na DNA.

IS dai ta taba kama yankuna da dama na arewa maso gabashin Syria da kuma arewacin Iraqi inda ta wanzar da mulki kan mutane kusan muliyan takwas.

A watan Disamban 2017 Iraqi ta ayyana cewa ta ci galabar IS tare da fatattakar ƙungiyar a sauran yankunan da take iko a 2019.

Sai dai kuma mayaƙan na ci gaba da kai hare-hare a sassan ƙasar musamman kan jami'an tsaron Iraqi