'Nakan ji kunyar shiga mutane saboda manyan nonuwana'

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Rebecca Thorn
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Global Health, BBC World Service
- Lokacin karatu: Minti 5
"Nakan riƙa tafiya kafaɗa ta a ɗage saboda nuna cewa ina da manyan nonuwa. Idan na tuna haka kunya kan kama ni."
A shekara ta 2010, wata farfesa a Argentina ta yanke shawarar zuwa a yi mata aiki don rage girman nononta.
Yanzu da take shekara 52, ta ce aikin da aka yi mata ya ba ta "wani ƴancin" da ba ta taɓa ji ba a baya.
Yayin da masu manyan nonuwa ke jan hankalin wasu mazan a sassan duniya da dama, ta wani ɓangare kuma yakan shafi lafiyar matan da kuma ingancin rayuwarsu.
An bayyana cewa manyan nonuwa na janyo wasu alamomi da dama ciki har da ciwon baya, ciwon kai, karkatar da jiki, rashin jin wani abu a jiki da kuma matsalar bacci, har ma da matsalar ƙwakwalwa.
Sabbin alkaluma daga ƙungiyar masu kwaskwarimar jiki ya nuna cewa an yi wa mata 652, 676 aikin rage girman nono a shekarar 2024
Brazil ce ke da yawan alƙaluma, inda take da 115, 647, sai Amurka mai 67, 478, Faransa 38,780, Jamus 32,068, Turkiyya 25, 334 sai kuma Indiya 22, 400.

Asalin hoton, Raquel
Raquel ta ce ta fuskanci matsalar ciwon baya saboda manyan ƙirji da take da shi tun tana budurwa.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Sai dai, ta ce ana ɗaukar masu manyan nonuwa a Argentina a matsayin ƴan albarka.
"Yawancin mutane, musamman mata za su faɗa miki cewa kin yi babbar sa'a," in ji ta.
"Na yi sa'a. Na sha wahala sosai lokacin da nake budurwa, da kuma a matsayin mace da kuma uwa."
Ta ce har yanzu tana fama da ciwon baya saboda yadda ta riƙa tafiya da ɓoye jikinta.
Raquel ta ce tana jin daɗin wasan yoga da kuma zuwa wurin motsa jiki. Sai dai, manyan nonuwanta sun hana ta motsa jiki.
Dakta Nora Nugent, shugabar ƙungiyar masu kwaskwarimar jiki a Birtaniya, ta ce taƙaita zirga-zirga da wahalhalu wajen motsa jiki na cikin ƙorafe-ƙorafe da take samu daga wajen mata masu zuwa don yi musu aikin rage nono.
"Manyan nonuwa na da nauyi, don haka ne ma za su iya jujjuyaka da kuma jawo ciwon baya da na wuya," in ji ta.
"Lamarin kuma yana hana mata sakewa wajen motsa jiki, kuma akwai wahala wajen samun rigar mama da za ta fi dacewa da su."
Raquel ta ce tana buƙatar saka "rigar mama biyu zuwa uku" domin tallafa wa nonuwanta. Kuma sai an biya ƙarin kuɗaɗe kafin samun rigar mama da za ta yi daidai.
"Rigar mama na manyan nonuwa a Argentina na da tsadar gaske," in ji ta.
'Na samu sake wa'

Asalin hoton, Raquel
Nugent ta ce an cire wa yawancin matan da ke zuwa wajenta a Birtaniya giram 500 zuwa 800 daga nonuwansu, duk da cewa ta ga abin da ya fi haka.
"Wasu lokuta ba shi da girman gaske a jiki, sai dai suna da girma ne a wani ɓangare karami," in ji ta.
Ga batun Raquel, likitoci sun cire kilogram 2.5 daga nonuwanta.
"Bayan yin aikin, na tuna abin da na ji bayan tsugunawa don ɗaukar abu a ƙasa, na ji wani irin sakewa a jikina. Na ji daɗi da sakewa mai kyau."
Alfanun rigar mama mai kyau
Lokacin da Farfesa Joanna Wakefield-Scurr ta je ganin likita domin tattauna kan zafin da take ji a mamanta, an ba ta shawarar cewa abin da take buƙata shi ne rigar mama mai kyau.
A matsayinta na ƙwararriya a ɓangaren tsarin yadda jiki yake aiki, ta yanke shawarar yin bincike don samun rigar mama mai kyau.
"Na gano cewa ba mu da masaniya kan abin da ya sa muke ɓuƙatar rigar nono, alfanun da rigar mama ke da shi, da kuma yadda zai yi aiki," in ji Wakefield-Scurr.
"Don haka, ana ɗaukar rigar mama a matsayin abin ƙawa maimakon wani abu mai amfani da kuma yake da alfanu na lafiya. Na yi bakin ciki da hakan."
Wannan ne ya ba ta ƙwarin gwiwar kafa ƙungiyar bincike kan lafiyar nono a Jami'ar Portsmouth a 2005.
Tawagarta ta yi duba kan wasu abubuwa huɗu marasa kyau na saka rigar mama da ba ta dace ba - zafi, karkatar da fata, sauyawar yadda ake numfashi da kuma tsawon lokaci na bugawar kirji.
"Idan kina da manyan nonuwa kuma suna tsalle sama da ƙasa, hakan zai sauya yadda kike numfashi. Yana kuma sauya irin ƙarfin da kike amfani da shi a ƙasa. Lamarin zai shafi ɗaukacin yadda jikinki ke kiki."

Asalin hoton, UEFA/UEFA via Getty Images
Bayan bincike na tsawon shekaru, tawagar ta gano salon yadda nono ke tafiya ta wasu ɓangrori takwas yayin kowane irin motsa jiki.
Sun bayyana cewa abin da ya fi dacewa wajen rage zafin nono, shi ne tafiya a hankali, maimakon duba yadda nonuwan suke.
A yanzu tawagar ta yi aiki da ƙwararrun ƴanwasa kamar tawagar mata ta Ingila Lionesses, da kuma manyan ƙwararrun ƴan wasan golf domin samar musu da rigar maman da ta fi dacewa.
"Muna ganin yadda hukumomi irinsu hukumar ƙwallon ƙafar Birtaniya da hukumar wasan zari-ruga ke zuba kuɗi wajen samar da kayakin lafiya ga ƴan wasa mata - kuma hakan ya kasance ne a shekaru biyar da suka wuce," in ji Wakefield-Scurr.
"Sabon abu ne, sai dai yana da kyau cewa muna ganin wannan sauyi."
'Marasa lafiya na son rayuwa cikin ƙoshin lafiya'
Yadda al'umma ke kallo da kuma fahimtar mata masu manyan nonuwa, abu ne da Raquel ta fuskanta.
Ta ce an riƙa mata gurguwar fahimta bayan aikin rage nonuwanta, kuma akwai rashin fahimta daga wurin wasu mutane.
"Ina tunanin mutane da dama sun ɗauki hakan a matsayin abun ƙawa maimakon batu na lafiya," in ji ta.
"Na tuna lokacin da aka yi min aiki, wata mata ta faɗamin cewa, 'Ya kamata ki je a rage miki ciki."
Raquel ta ce ba ta yi nadama ba duk da irin waɗannan abubuwa.
"Ina cikin farin ciki kuma yanzu da yake na daina yin al'ada, ban san yadda zan yi rayuwa da manyan nonuwa ba. Ba zan iya tunanin kallon kaina da wancan nauyi ba."
Dakta Nugent ta ce ƙaruwar matan da ke neman rage nonuwansu, na nuna yadda kula da kai tsakanin mutane ke ƙara girma.
"Akwai ƙaruwar marasa lafiya da ke son ganin sun rayu cikin ƙoshin lafiya, ba mata kaɗai ba," in ji ta.











