Abubuwa bakwai da Trump ya ce zai yi a matsayin shugaban Amurka

Bayanan bidiyo, Ga Buhari Fagge da bayani kan alƙawurran na Trump
Abubuwa bakwai da Trump ya ce zai yi a matsayin shugaban Amurka

Donald Trump zaɓaɓɓen shugaban Amurka ce zayyana wasu abubuwa guda bakwai da ya ce zai mayar da hankali a kai ciki har da batun 'yan cirani, da tattalin arziki, da yaƙin Ukraine.

Da alama ya samu ɗimbin magoya baya sakamakon manufofinsa na siyasa, musamman a majalisar dokokin ƙasar bayan da jam'iyyarsa ta Republican ta sake ƙwace iko da majalisar dattawan ƙasar.

A jawabin murnar lashe zaɓe da ya gabatar, Mista Trump ya sha alwashin ''yin mulkin bisa taken: 'Cika alƙawuran da muka ɗauka'.

Amma a wasu fannonin, ya bayar da taƙaitaccen bayanin yadda zai cimma manufofin nasa.