Hukumar da ke tabbatar da zaman lafiya tsakanin Musulmai da Kirista a Jos

Bayanan bidiyo, Hukumar da ke tabbatar da zaman lafiya tsakanin Musulmai da Kirista a Jos
Hukumar da ke tabbatar da zaman lafiya tsakanin Musulmai da Kirista a Jos

Danna hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Filato na daya daga cikin jihohin Najeriya da ke fama da rikicin addini.

Rikicin ya yi mummunan tasiri ga dukkan bangarorin addinan biyu, tare da asarar rayuka da dukiyoyi.

A yanzu Musulmai da Kiritoci sun samar da wata cibiya da nufin farfado da zaman lafiya tsakanin bangarorin biyu a kasar.

Ƙungiyar mai suna Peace Building Agency, ta samu nasarori sosai a ƙoƙarinta na farfaɗo da zaman lafiya a wasu sassan jihar.

A wata ziyara da BBC ta kai a baya-bayan nan, abokin aikinmu Mukhtar Adamu Bawa ya tattauna da shugabannin ƙungiyar kan yadda take aiki.