Dan Aliyu da Dogon Dogo sun tashi canjaras a Maraba

Damben gargajiya

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 1

An tashi canjaras tsakanin Dan Aliyu da Dogon Dogo Mai Takwasara a damben gasa ranar Lahadi a damben safe.

Tun farko an tsara karawa tsakanin Dogo Mai Takwasara Guramaɗa da Alasan Garkuwan Bahagon Ƴansanda daga Jamus, amma ba a samu damar yin damben ba.

Hakan ya faru ne sakamakon rashin lafiyar Alasan, dole aka hakura da damben da aka tsara a Ƴan tifa a karammar hukumar Karo a jihar Nasarawa, Najeriya.

Dalilin haka ne aka haɗa damben Dan Aliyu a madadin Alasan da kuma Dogon Dogo a maimakon Mai Takwasara.

Dan Aliyu daga Jamus ya buga turmi biyu da Dogon Dogo Mai Takwasara Guramaɗa ba tare da damben ya fitar da gwani ba.

Tun kafin damben gasa an kara tsakanin Dogon VIO Guramaɗa da Dan Aliyu daga Jamus, inda Guramaɗa ya yi nasara a turmi na biyu.

Haka shima Dogon Dogon Mai Takwasara ya buge Shamaki daga Arewa a turmi na biyu.

An kuma yi canjaras ba kisa tsakanin Korona daga Kudu da Shagon Inda daga Jamus da na Sabon Gundumi Guramaɗa da Shagon Nokia daga Arewa.

A damben na ranar Lahadi an yi wa Najib da Koso ajo, waɗanda dukkansu daga Arewa suke.