Kun taba sanin wani goro da ake kira goron Tula?

Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon
Kun taba sanin wani goro da ake kira goron Tula?

Goron Tula wani nau’in dan itace ne mai kama da kanya a ido sannan yana da kwallaye da kuma zaki kamar sukari.

Ana dai noma wannan nau’in goro a garin Tula da ke jihar Gombe.

Ana sayar da mudun goron Tula naira fiye da dubu 50, abin daya sa itacen ya zama abin alfahari ga al’ummar yankin.

A wannan bidiyo, manoman goron sun yi cikakken bayani dangane da muhimmancinsa da suka hada da gyaran gida ga ‘ya’ya maza.