Na ji sassauci bayan yanke masa hukuncin kisa - Mahaifiyar Hanifa

Bayanan bidiyo, Danna hoton sama ku kalli bidiyo:
Na ji sassauci bayan yanke masa hukuncin kisa - Mahaifiyar Hanifa

Mahaifiyar Hanifa Abubakar, yarinya mai shekara biyar da malaminsu ya kashe, na so gwamnati ta gaggauta zartar wa mutumin mai suna Abdulmalik hukuncin kisa da kotu ta yanke masa.

Cikin wata hira ta musamman da BBC Hausa, Murja Sulaiman Zubair ta ce "bayan yanke hukunci na ji sassaucin wani abin kuma alhamdulillahi".

Shi ma mahaifin Hanifa, Abubakar Abdulsalam, ya ce ya samu natsuwa "tun da an yanke masa hukunci daidai da abin da ya aikata", kuma ya gode wa mutane bisa addu'o'in da suka yi musu.

Babbar kotun da ke Jihar Kano a arewacin Najeriya ta yanke wa Abdulmalik hukuncin kisa ne ta hanyar rataya bisa laifin kashe Hanifa da kuma ɗaurin shekara biyu kan laifin garkuwa da ita.