'Fursunoni 443 sun tsere daga gidan-yarin Kuje'

Hukumomi sun ce lamarin bai shafi manyan mutanen da ke daure a kurkukun ba

Hukumar da ke lura da gidajen-yari a Najeriya ta ce fursunoni 879 ne suka tsere yayin harin da aka kai kurkukun Kuje da ke Abuja ranar Talata da daddare.

Sanarwar da mai magana da yawun gidan-yarin, Abubakar Umar ya sanya wa hannu, ta ce wasu fursunoni sun koma don radin kansu amma kawo yanzu ana neman fursunoni 443.

Tun da farko Ministan Tsaron Najeriya, Bashir Magashi, ya ce kimanin fursunoni 600 ne suka tsere a yayin harin da aka kai gidan-yarin na Kuje.

Ministan, wanda ya tabbatar wa BBC wannan labarin, ya kara da cewa kusan 300 daga cikinsu sun mika kansu ga hukumomi don radin kansu yayin da jami'an tsaro suka kamo wasu daga cikinsu.

Ministan ya dora alhakin harin kan kungiyar Boko Haram, yana mai cewa akwai kimanin mayakan kungiyar akalla 64 a gidan-yarin lokacin da aka kai harin.

Magashi ya kuma tabbatar da mutuwar jami'in Civil Defence daya.

Ministan ya ce mayakan Boko Haram ne suka kai harin

Sai dai Abubakar Umar ya ce fursunoni hudu sun mutu yayin da 16 suka jikkata yayin harin.

Hukumomi sun ce a halin yanzu komai ya lafa a gidan-yarin kuma jami'an tsaro sun sake karbe iko da kurkukun.

Harin na zuwa ne 'yan sa'o'i bayan da 'yan bindiga a Katsina suka yi wa kwambar motocin Shugaba Muhammadu Buhari kwanton-bauna a kan hanyarsu ta zuwa garin Daura, mahaifar shugaban kasar.

Shin Abba Kyari ya tsere daga kurkuku?

A gidan-yarin na Kuje ne ake tsare da manyan mutane da 'yan siyasa da masu tayar da kayar baya, ciki har da Abba Kyari, mataimakin Kwamishinan 'yan sandan da ake zargi da hannu a safarar miyagun kwayoyi.

Kuma jama'a da dama sun rika tambaya kan ko yana cikin wadanda suka tsere.

Sai dai magana da yawun gidan-yarin, Abubakar Umar, ya shaida wa BBC cewa jam'in 'yan sandan na nan a gidan-yarin cikin koshin lafiya.

Ya ce maharan ba su je inda ake tsare da shi ba.

"Muna shaida wa jama'a cewa DCP Abba Kyari da sauran manyan mutanen da ke tsare a kurkuku ba su tsere ba. A halin yanzu suna nan a tsare cikin koshin lafiya," in ji Umar.