Zanga-zangar da 'yan ƙwadago suka yi a sassan Najeriya
Zanga-zangar da 'yan ƙwadago suka yi a sassan Najeriya
Zanga-zangar ƙungiyoyin ƙwadago a Najeriya ta durƙusar da harkoki da dama ranar Laraba a wasu sassan ƙasar. 'Yan ƙwadago a jihohi da dama sun gudanar da maci, inda suka riƙa alluna da ƙyallaye da tutoci don nuna adawa da halin matsin rayuwa da kuma hauhawar farashi.
'Yan ƙwadagon dai na wannan zanga-zanga ne saboda matakin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu na janye tallafin man fetur, wanda aka yi imani ya haddasa tsadar rayuwar da ake fuskanta yanzu a ƙasar.




