Yadda za ku tantance abubuwan da aka haɗa da AI da na gaske
Yadda za ku tantance abubuwan da aka haɗa da AI da na gaske
Zamani ya kawo lokacin da jama'a musamman gwanayen amfani da basirar AI wajen haɗa abubuwan ƙarya da na jabu ke ƙirƙirar maganganu da hotuna da bidiyon bai taɓa faruwa ba da sunan abin da ya faru.
A wani ɓangare na BBC na ƙaryata labaran ƙarya, kafar na ci ga ada yin duk abin da ya kamata wajen yaƙar labaran ƙarya da na ƙanzon kurege domin wayar da jama'a.
A wannan bidiyon, ma'aikacin BBC, Aminu Kutama ya yi mana duba kan yadda za ku tantance abubuwan da aka haɗa da ƙirƙirarriyar basirar AI da na gaskiya.



