Dubban jama'a sun sake zanga-zangar kin jinin gwamnatin Trump a Amurka

Asalin hoton, Reuters
Ana sake gudanar da manyan zanga-zanga a manyan biranen Amurka a kan nuna adawa da tsare -tsare da manufofin gwamnatin Donald Trump.
Masu zanga-zangar sun riƙa rera waƙoƙi na suka tare da ɗaga kwalaye masu rubutu daban-daban na suka da zargin gwamnatin da keta haddin kundin tsarin mulki da 'yancin jama'a.
Wannan shi ne karo na biyu a wannan wata da dubban mutane suka yi tattaki a titunan Amurka domin nuna bacin ransu kan yadda Shugaba Donald Trump ke gudanar da mulkin kasar.
Wasu daga cikin abubuwan da suke korafi a kai sun hada da fitar da baki daga kasar da korar ma'aikata da gwamnati ke yi da kuma zargin tauye 'yancin fadin albarkacin baki.
Wani daga cikin masu zanga-zangar ya yi korafi da cewa: '' Gwamnatin Trump na son kafa kasa ta kama-karya a Amurka inda bangaren zartarwa ke iko da duka bangarorin gwamnati uku kuma yawancin mutane ba sa lura da hakan.''

Asalin hoton, Getty Images
Haka kuma masu zanga-zangar na nuna bacin rai sosai kan irin ikon da Trump ya bai wa attajirin duniya mai kamfanin Tesla - Elon Musk, wanda ya kori ma'aikatan gwamnati sama da dubu 200, ya kuma rushe hukumomin agaji na Amurka da dama da ke fgadin duniya.
Masu zanga-zangar sun nuna bacin ransu a kan hakan inda suka yi gangami a kofar kamfanin sayar da motocin na Tesla a Amurka.
An tsara zanga-zangar da aka yi wa lakabi da "50501", domin "zanga-zanga 50 , jihohi 50 , gangami1 ", ta yadda za ta zo daidai da lokacin tunawa da fara yakin juyin-juya-hali na Amurka na 250.

Asalin hoton, Getty Images
Parade goers in Lexington, Massachusetts
An yi asarar biliyoyin dala a kasuwart hannun jari a duniya lokacin da ya kara haraji a kayan da ake shigarwa Amurka daga kasashen duniya musamman ma na kasar China, sannan darajar dala ta sulmuyo kasa, abin da ya karya gwiwar masu zuba jari.
Masana tattalin arziki sun ce masu sayen kaya a Amurka za su dandana kudarsu a kan karin harajin na Amurka - inda za su rika sayen kaya da tsada - kuma wannan ana ganin na daga cikin abubuwan da suka sa wasu daga cikin 'yan kasar ta Amurka ke nuna adawa da gwamnatinsa da kuma da-na-sani-kan sake zabensa.
Ba shakka, abu ne mawuyaci a ce ba a ga wani gagarumin sauyi ba a wata uku na farko na mulkin Donald Trump.











