Matashiya mai zanen ban kasa daga arewacin Najeriya

Bayanan bidiyo,
Matashiya mai zanen ban kasa daga arewacin Najeriya

Matasa a fadin arewacin Najeriya suna ci gaba da rungumar sana'o'i da ayyuka iri daban-daban a rayuwa, ciki har da zane, wanda ba kasafai mutane ke kallo da muhimmanci ba.

Al'ummomi da dama na amfani da zane wajen nuna wa sauran duniya al'adu da tsarin rayuwarsu da al'amuran da suka zamantakewa da tattalin arziki.

Wata matashiya daga arewacin Najeriya da ke baje-kolin baiwar zane don fito da baiwar halittun ban kasa da ke yankin ita ce, Aisha Mohammed Buba Mashio.

Ku kalli bidiyon matashiyar a nan sama.