Rayuwar Hausawa mazauna Obudu
Rayuwar Hausawa mazauna Obudu
Akwai al'ummar Hausawa fiye da dubu shida da ke zaune a garin Obudu na jihar Cross River da ke kudu maso kudancin Najeriya.
Tarihi ya nuna cewa Hausawa sun fara zama a garin tun fiye da shekara 100 da suka gabata, tare da gudanar da sana'o'i daban-daban a garin.
Jama'ar Hausawa na rayuwa a yankin ne tamkar suna zaune a arewacin Najeriya.



