Ban san dalilin da ya sa aka cire sunan Aminu Masari daga jerin ministoci ba - Dikko Radda

Bayanan bidiyo,
Ban san dalilin da ya sa aka cire sunan Aminu Masari daga jerin ministoci ba - Dikko Radda

Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umar Radda ya ce sunan tsohon gwamnan jihar, Aminu Bello Masari na daga cikin jerin wadanda ya tura fadar shugaban kasa domin nadawa a matsayin minista daga jihar Katsina, sai dai bai san me ya sa aka cire sunan Masari daga wadanda za a bai wa mukamin ba.

Ya ce “shugaban kasa ya bukace mu a matsayinmu na gwamnoni domin mu bada sunan mutum uku domin ya zaba, kuma na bada sunan mutum uku, wadannan su ne wadanda Allah Ya zaba.”

Ya kara da cewa “na gabatar da sunan tsohon gwamnanmu Aminu Bello Masari, shi ne na farko, sai Hannatu Musawa ita ce ta biyu, sai kuma Arc Ahmed Musa Dangiwa shi ne na uku.”

Sai dai ya ce bai yi tsammanin ma jihar Katsina za ta samu guraben ministoci har biyu ba, amma sai ga shi shugaba Tinubu ya bai wa jihar.

Rashin bayyanar sunan tsohon gwamnan na Katsina, Aminu Masari a jerin ministoci daga Katsina ya zo wa mutane da dama da mamaki, ganin irin tasirinsa a siyasar jihar.

A bangaren tsaro kuwa, a kwanan baya ne, gwamnan ya kaddamar da rukunin farko na matasa 'yan sintiri su 1,500 don tallafawa dakarun tsaron Najeriya, wajen tsare garuruwa da kauyuka daga hare-haren 'yan fashi.

Rikicin 'yan fashin daji, babbar matsalar tsaro ce a Najeriya, da akasari take addabar jihohin arewa maso yamma, inda 'yan bindiga a kan babura suke kai hare-hare, da sace mutane don neman kudin fansa.

A wannan zantawar da BBC Hausa, gwamnan na jihar Katsina ya yi bayani a kan batutuwa da dama ciki har da samar da tsaro da ilmi da lafiya, kimanin wata shida bayan hawansa kan karagar mulki.