Guguwar Ian: 'Babu abin da muke so kamar wutar lantarki'
Guguwar Ian: 'Babu abin da muke so kamar wutar lantarki'
An gudanar da zanga-zanga a Havana, babban birnin Cuba, bayan mahaukaciyar guguwar Ian ta lalata dukkan hanyoyin samar da lantarkin kasar ranar 27 ga watan Satumba.
Bangarorin birnin da aka dawo da wutar lantarki ba su da yawa, abin da ya sa mutane suka shiga zanga-zanga a cikin duhu domin kira ga gwamnati ta dawo da hasken lantarki.



