Burin 'yan Kogi ga zaɓabɓen Gwamna Usman-Ododo
Burin 'yan Kogi ga zaɓabɓen Gwamna Usman-Ododo
Al'ummar jihar Kogi suna ci gaba da tofa albarkacin bakinsu tun bayan sanar da mutumin da ya lashe zaɓen gwamna a jihar da ke arewa maso tsakiyar Najeriya.
Ahmed Usman-Ododo dai ya lashe zaɓen na ranar Asabar da ta wuce ne da yawan ƙuri’a 446,237, inda ya doke babban abokin takararsa, Muritala Ajaka na jam’iyyar SDP, da ya samu ƙuri’a 259,052.
Ga abin da mazaunan jihar suka shaida wa BBC game da fatan da suke da shi ga zababben gwamnan.



