'Abin da ya sa muke so a zaɓi Akpabio shugaban Majalisar Dattijai'

Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyo
'Abin da ya sa muke so a zaɓi Akpabio shugaban Majalisar Dattijai'

Jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya ta fitar da wata sanarwa inda ta bayyana sunayen Sanata Godswill Akpabio da Barau Jibrin a matsayin waɗanda ta zaɓa domin jagorancin Majalisar Dattijai da za a ƙaddamar nan ba da jimawa ba.

Hakan na zuwa ne bayan da aka yi ta samun ce-ce-ku-ce game da wanda ya kamata ya riƙe muƙamin.

A cikin wannan bidiyo, Sanata Bashir Garba Lado, ya bayyana wa BBC abubuwan da jam'iyyar ta duba kafin ayyana Sanata Akpabio a matsayin wanda take son ya zama shugaban majalisar dattijan ta Najeriya.