Dole shugabanni mu faɗa wa junanmu gaskiya - Gwamnan Filato
Dole shugabanni mu faɗa wa junanmu gaskiya - Gwamnan Filato
Gwamnan jihar Filato, Caleb Muftwang ya ce an kama mutanen da ake zargi da kashe wasu matafiya a garin Mangu na jihar kwanakin baya.
Muftwang ya ce dole shugabanni su faɗa wa junansu gaskiya dangane da matsalolin da ke tsakanin al'umma.
Gwamnan ya ce tashin hakanlin da ake samu a jiharsa, abu da aka jima ana fama da shi.
Ya ƙara da cewa gwamnatocin baya sun sha kafa kwamitoci da suka gudanar da bincike da dama da nufin magance matsalar tsaron jihar, ammm har yanzu haƙa ba ta cimma ruwa ba.
''Rashin hukunta waɗanda aka samu da laifi ne ke ƙara assasa rikicin da ake yawan samu a jihar Filato'', in ji shi.
Mista Muftwang ya ce rikicin manoma da makiyaya da ake fama da shi a jihar tun yana yaro ake yinsa.



