...Daga Bakin Mai Ita tare da Maryam Jos
...Daga Bakin Mai Ita tare da Maryam Jos
A wannan mako cikin shirin Daga Bakin Mai Ita mun kawo muku tattaunawa da tauraruwar fim ɗin Hausa Maryam Jos.
Maryam, wadda aka haifa a birnin Jos ta bayyana yadda ta fara yin aiki kyauta domin neman cika burinta na zama tauraruwa a fina-finan Hausa.
Ta kuma ce ta fuskanci ƙalubale da dama kafin daga bisani ta yi dace.
Ɗaukar hoto: Umar Laddu



