Ina mafita ga sojojin da ke mulki a Mali bayan boren 'yan bindiga?

    • Marubuci, Makuochi Okafor
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Africa
    • Marubuci, Mohamed Ibrahim
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Arabic
  • Lokacin karatu: Minti 5

Ba za a iya misalta ɗimuwar da aka shiga ba a duka Yammacin Afrika bayan harin da mahara suka kai cikin tsari wanda ya haɗa da babban birnin Mali Bamako, ya kai ga kisan gillan ministan tsaron ƙasar tare da karɓe iko da yankin arewaci.

'Yan Mali da ke zaune a garuruwa da dama sun tashi da jin ƙarar harbe-harbe da tashin bama-bamai a safiyar Asabar - cikin wani harin haɗin gwiwar da ƙungiyoyin yan ta'adda biyu da suka haɗa da ƙungiyar 'yan aware ta Azawad Liberation Front (FLA) da kuma ta JNIM da ke da alaƙa da alƙa'ida suka yi iƙirarin ɗaukar alhaki.

Girman hare-haren da kuma ficewar sojin Mali da na Rasha daga garin Kidal da ke arewacin ƙasar - da kuma karɓe iko da ƙungiyoyin 'yan awaren suka yi, ya janyo ana ta sa ayar tambaya kan ƙarfin da gwamnatin sojin da Kanar Assimi Goita ke da ita, wadda ta karɓi iko a juyin mulkin da ta yi a Agustan 2020.

Sai da aka ɗauki kwanaki kafin Assimi Goita ya bayyana a bainar jama'a tun bayan harin da aka kai, wanda ya janyo ake tambayar yaya goben sojin da ke mulki a Mali, da kuma rawar da sojin Rasha da makwabtan Mali za su taka kan barazanar tsaron da ƙasar ke fuskanta.

Mene ne zai faru a nan gaba?

Hasashen farko: sojoji su ci gaba da mulki su yaƙi 'yan aware

Mafiya yawan masu sharhi na ganin wannan nasarar da suka samu ta ɗan gajeren wa'adi ce, saboda har yanzu sojoji ne ke riƙe da iko da manyan biranen ƙasar da kuma cibiyoyin gudanarwa.

Amma suna cewa nan da 'yan kwanaki abubuwa za su zama sun yi wa 'yan aware wuya saboda sojoji za su kai harin ramuwa kan JNIM da kuma FLA.

Nasara ko akasinta ne zai nuna "yiwuwar ci gaba da mulkin sojojin", kamar yadda Beverly Ochieng wani kwararran mai sharhi na kamfanin Control Risks ya bayyana.

Kwanaki uku bayan harin Kanar Goita ya yi bayani a gidan talabijin na ƙasar, inda ya ce tuni sun shawo kan lamarin, tare da ɗaukar alƙawarin maganin waɗanda suke da hannu cikin wannan hari.

Tun da fari sai da shafin kafar yaɗa labarai na fadar shugaban ƙasa ya wallafa hoton Goita na tattaunawa da jakadan Rasha a Mali, Igor Gromyko, wani mataki mai muhimmanci da sojojin mulki suna nuna na cewa ƙawancensu har yanzu yana nan.

Kazalika sun wallafa hoton shugaban juyin mulkin ya kai ziyara asibitin da aka kwantar da waɗanda suka raunata yayin harin.

Masu sharhi na ganin cewa kisan da aka yi wa ministan tsaron ƙasar Sadio Camara zai iya raunata shirin sojin na kai harin ramuwa.

Camara na daga cikin mutane masu ƙarfin iko a tsarin gwamnatin, "kuma shi ne ya ba da shawarar kawo sojin haya na Rasha zuwa kasar ta Sahel", in ji Ulf Laessing, na ƙungiyar Konrad Adenauer Foundation.

Yayin da soji Mali ke cewa suna yaƙi domin tseratar da manyan yankunan ƙasar, su kuma 'yan aware na cew suna son mamaye kudancin ƙasar daga Kidal a nan gaba.

"Muna son karɓe iko da birnin Gao. An cimma duk wata ƙofa ta Gao, amma har yanzu sansanin sojinmu na nan kalau," inji kakakin gwamnatin Mohamed Elmaouloud Ramadane.

Ya ƙara da cewa babban birnin nan mai tarihi Timbuktu yana kan idonsu: "Yana da sauki mu karɓe su da zarar mun karɓe iko da Gao da Kidal ba ki ɗaya."

Sojojin sun samu goyon bayan 'yan ƙasa lokacin da suka amshe iko kimanin shekaru shida baya, sun yi alƙawarin kawo ƙarshen matsalar tsaron da Mali ta daɗe tana fama da shi.

A yanzu ƙungiyar JNIM ta tura ta zuwa matsayin kare kai da sanya shinge ababan hawa a babban birnin ƙasar, yayin da masu riƙe da bindiga ke ci gaba da haifar da fargaba da koma bayan tattalin arziki.

Hasashe na biyu: Sojoji za su ci gaba da mulki da taimakon sojin Rasha amma dole su sauya sabon salo

Harin da aka kai a arshen satin ya taɓa ƙimar Rasha a matsayin ƙawa abar dogaro a Mali, in ji Ochieng.

Bayan karɓe iko da sojoji suka yi a farkon shekarun 2020, an shaida wa sojojin Faransa da suke taimakawa Mali su fice da kasar sannan na Rasha suka zo suka maye gurbinsu domin kawo ƙarshenrashin tsaro a Mali.

Ƙimar Rasha ta matuƙar taɓuwa bayan gazawar da aka samu wajen kare manyan biranen ƙawayenta, in ji Laessing.

Yayin da ta nace kan neman taimakon sojin Rasha, Mali za ta buƙaci faɗaɗa harkokin sojinta da ƙawancenta.

Wani zaɓi da ke hannunta a yanzu shi ne ƙawace da Turkiyya, wadda ke fatan faɗaɗa ikonta a nahiyar Afrika.

Ochieng ya ce akwai rahotanni da ke cewa an kai jami'an tsaron Tukiyya Mali "domin horas da masu gadin fadar shugaban ƙasar".

Tuni Turkiyya na da alaƙar tsaro da Mali, ta riƙa taimaka mata da jirage marasa matuƙa har ta sake karɓe iko da Kidal daga 'yan tada ƙayar baya a 2024.

Mali kuma ta nuna alamun sabunta alaƙa da Amurka bayan shekaru na warware alaƙa.

A farkon wannan shekarar Nick Hocker shugaban sashen harkokin cikin gida na Amurka ɓangaren Afrika, ya je Bamako domin nuna amincewa da 'yancin Mali, tare da bayyana wasu sharuɗai da za su jaddada alaƙarsu, lokacin da ake tsaka da watsar da tsofaffin manufofi.

Ya jaddada buƙatar aiki tare kusa da kusa tare da Mali da ƙawayenta, Burkina Faso da Niger, kan harkokin tsaro da na tattalin arziƙi.

Bamakon za ta ƙara dogara ne kan ƙungiyar ƙawayenta na Sahel AES, wadda ta haɗa da Mali da Nijar da Burkina Faso, waɗanda gwamnatin soji ne duka ke jagoranta.

Ƙungiyar ta nemi taimakon Mali, duk da cewa har yanzu ba su yi wani aikin yaƙi tare ba.

A wajen Rasha tambayar ita ce, ko za ta iya ci gaba da riƙe girmenta a idon Mali bayan ta yi yunƙurin fadada ƙawance tsaronta.

Wannan rikici zai iya zama zakaran gwajin dafi na faɗaɗa dabarunta a Afrika, inda Moscow ke faɗaɗa ikonta ta fuskar aikin soji.

Hasashe na uku: Matsi ya kori sojojin Mali daga mulki - to amma wane ne zai ci gaba da mulkin?

Harin ranar Asabar ya haifar da wani gagarumin ƙalubale ga sojojin da suke mulki na tsawon shekaru.

Idan hare-haren suka ci gaba matsin lamba kan gwamnatin soji zai ƙaru.

Wani abun da zai iya ƙara faruwa shi ne a ƙara wani juyin mulki, wasu sojin na daban su karɓe iko.

Wani abu da zai iya faruwa shi ne, ƙawancen FLA-JNIM ya maye gurbin gwamnati mai ci sai dai kuma za ta fuskanci matsalolin cikin gida daban-daban.

FLA ta gabatar da kanta a matsayin ƙungiyar siyasa da kishin ƙasa, yayin da ita kuma JNIM take matsayin ƙungiya masu kishin Islama.

'Yan adawar Mali da masu kishin addini sun taɓa rikici a baya a 2012, lokacin da masu kishin suka amshe iko a hannun 'yan ƙabilar Tuareg.

Wani kakakin FLA ya ce su da JNIM yan uwa ne, yana cewa maƙiyinsu ɗaya ne, dan haka ya kamata mu kasance ƙarƙashin inuwa ɗaya.

Amma shugaban FLA Sayed Bin Bella ya shaida wa BBC "babu haɗaka".

Wannan banbancin zai iya haifar da rashin fahimta da jituwa da tsakanin ɓangarorin biyu.