Ashley Young ya sanar da yin ritaya daga taka leda, Premier League
Tsohon ɗan wasan tawagar Ingila, Ashley Young ya sanar da yin ritaya daga buga ƙwallon ƙafa yana da shekaru 40.
Young ya fara takal eda a Watford daga nan ya koma Aston Villa da Manchester United da Inter Milan da kuma Everton.
Ya rataye takalmansa a Ipswich Town, bayan da ya koma ƙungiyar kan yarjejeniyar kaka ɗaya a watan Yulin 2025, bayan da yarjejeniyarsa ta karkare a Everton.
Young ya fara buga wa Ingila wasa ne a watan Nuwamban 2007, kuma ya buga mata wasa 39 da cin ƙwallo bakwai.
Ya fara zama kwararren ɗan wasa a Watford a 2003, sannan ya lashe Premier League da UEFA Europa League da FA Cup da EFL Cup tare da Manchester United, sannan ya ɗauki kofin Serie A a lokacin da yake Inter Milan.
Ya buga wasa 13 kacal a Ipswich, inda 10 daga cikinsu ya shiga ne a matsayin canji.