Makaman da aka yi amfani da su wajen kashe dubban masu zanga-zanga a Iran

Asalin hoton, Mamlekate
- Marubuci, Farzad Seifikaran
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Persian Forensic
- Lokacin karatu: Minti 6
"An yi ta jin karar harbin bindigogi kafin dare ya gitta har zuwa tsakiyar dare. Abin ya kasance tamkar fagen yaki. Babu kakkautawa. Lokacin da na fita waje washegari, jini ne ke ta kwarara - a gefen hanya, kan tituna da kuma bangon wurare... ko'ina ya baci da jini."
Wannan wani ganau ne daga birnin Kermanshah na Iran ke kwatanta yadda jami'an tsaro suka yi dirar mikiya kan al'ummomin Dara Derizh ranar 8 ga watan Janairu yayin tattaunawa da BBC.
Jim kadan kafin gwamnati ta katse hanyoyin intanet a fadin kasar, hotunan bidiyo sun karade shafukan sada zumunta, inda suke nuna masu zanga-zanga kwance cikin jini a yankin bayan harbin jami'an tsaro. Daga nan, komai ya zama duhu.
Wannan sabuwar zanga-zanga a Iran, wadda ta soma sakamakon karyewar darajar kudin kasar da kuma tsadar rayuwa a karshen watan Disamba, ta rikide zuwa gagarumar zanga-zangar kin jinin gwamnati.
Murkushe masu zanga-zanga da jami'an tsaro suka yi ranar 8 da 9 ga watan Janairu, ya janyo tashin hankali da ba a taba ganin irinsa ba a tarihin Iran.
Rahotanni sun bayyana cewa an kashe masu zanga-zanga a yawancin birane 200 da zanga-zangar ta barke.
Yayin da ya kasance babu ainihin alkaluman wadanda aka kashe, murkushe masu zanga-zangar ta hanyar amfani da muggan makamai wanda aka gani a cikin hotuna, da bahasin shaidu da kuma rahotannin da kungiyoyin kare hakkin dan'adam da yan jarida suka tattara, sun nuna cewa an kashe dubban mutane a fadin kasar.

Asalin hoton, Social media via Reuters
Bayan jin shiru na tsawon kwanaki biyu sakamakon katse hanyoyin intanet da na sadarwa da gwamnati ta yi, duniya ta kadu matuka da ganin hotunan gawawwaki cikin jakukkuna da aka kwantar a wajen cibiyar lafiya na garin Kahrizak, a Tehran.
Yawancin jakukkunan sun kasance a bude, inda ake iya ganin gawawwakin wasu ma babu komai a jikinsu inda jini yake ta kwarara a kasa, yayin da iyalai ke cikin kaduwa da kuma duba 'yan uwansu.
"Wannan shi ne gagarumin kisa da aka taba yi a tarihin Iran kuma daga daga cikin mafi girma a duniya." a cewar Payam Akhavan, wani tsohon mai shigar da kara na MDD a kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ICC, da ke birnin Hague, kamar yadda ya shaida wa BBC.
Gwamnatin Iran ta ce "masu zanga-zanga da 'yan ta'adda" sun yi ta bude wa jami'an tsaro wuta - da kuma fararen hula.
Amma bayan hasashe kan daruruwan bidiyo da hotuna, BBC ta tabbatar da girke jami'an tsaro da kuma makamai da dama, makaman sun hada da:
- mashinga
- bindigogin harbin labe
- bindigogin yaki
- gajerun bindigogi
- bindigogin pistol
- hayaki mai sa hawaye
- adduna
- wukake
- kulake

Asalin hoton, Vahid Online / Fars News Agency
Hotunan bidiyo daga birane irinsu Tehran, Isfahan, Yazdanshahr, da kuma Shahsavar wadanda BBC ta tantance, sun nuna manyan makamai, har da mashinga kan motocin jami'an soji.
An ruwaito cewa jami'an tsaro sun yi amfani da wadannan makamai wajen dakile masu zanga-zanga tare da yin kawanya.
Wani dandali a shafin Telegram ya wallafa wasu hotuna biyu na wata mota mai launin baki wadda ke dauke da mashinga a birnin Tehran, ranar 8 ga watan Janairu.

Asalin hoton, Iran International
Wani bidiyon zanga-zangar na ranar 9 ga watan Janairu a lardin Isfahan wanda gidan talabijin na Iran ya wallafa, ya nuna yadda ake bude wuta kan masu zanga-zanga ta hanyar amfani da mashinga.

Asalin hoton, Mamlekate
Bindigogin harbin labe

Asalin hoton, Obtained by BBC News Persian Forensic
Shaidun gani sun fada wa BBC cewa an yi amfani da bindigogin harbin labe a zanga-zangar ta watan Janairu, kuma an tabbatar da hakan ta hanyar kallon hotunan bidiyo da aka fitar.
Daya daga cikin bidiyon da BBC ta tantance na zanga-zangar ranar 9 ga Janairu a birnin Mashhad, ya nuna wasu mutum biyu sanye da kakin dakarun juyin juya-hali kan saman wani otel rike da bindigogin harbin labe.
A wata tataunawa da gidan talabijin na Iran, wani kwararren likita ya tabbatar da cewa 'yan ina-da-kisa sun kashe masu zanga-zanga. Ranar 8 ga Janairu, dan uwan Ebrahim Pourahmadian daga lardin Kurdistan wanda yake aiki a matsayin mai sa ido na wani gini a Tehran, ya fada wa BBC cewa wani dan ina-da-kisa ya harbe shi a kai, a gabansa dansa. Kuma hotunan da BBC ta samu daga binciken gawar Pourahmadian sun tabbatar da raunin harbin, a tsakiyar goshinsa.
Bindigogin yaki

Bindigogin yaki sun kasance manyan makamai wadanda dukkan sojoji da sauran jami'an tsaro ke amfani da su a Iran. Kuma BBC ta yi nazari kan hotunan bidiyo da dama wadanda ke nuna 'yansanda da dakarun juyin juya-hali na amfani da AK-47 da kuma sauran kananan bindigu da ake samarwa a kasar.
Wani bidiyo daga birnin Amol ya nuna jami'in tsaro na bude wuta kan masu zanga-zanga.
Gajerun bindigogi

Asalin hoton, Vahid Online
Binciken BBC ya tabbatar da cewa an yi amfani da gajerun bindigogi sosai.
Hotunan bidiyo daga birnin Lordegan ranar 1 ga Janairu da kuma birnin Abadan ranar 7 ga Janairu, sun nuna 'yansanda rike da gajerun bindigogi kan tituna lokacin zanga-zanga.
Kuma an gano amfani da irin wadannan bindigogi da dama, ciki har da wanda aka kera a Iran.

Asalin hoton, Obtained by BBC News Persian Forensic
Kamar yadda muka gani lokacin murkushe zanga-zangar mata a 2022, amfani da gajerun bindigogin a watan Janairu ya janyo kisan masu zanga-zanga da dama da kuma jikkata dubbai, inda yawanci suka matsala a idanu.
Tsakanin 9 da 10 ga Janairu, kusan marasa lafiya 1,000 ne suka bukaci kulawar gaggawa kan matsalar idanu wanda sinadari suka janyo, kamar yadda Dakta Ghasem Fakhraei shugaban asibitin ya fada wa wani kamfanin dillancin labarai a Iran.
Bindigogin pistol
Wasu hotunan bidiyo biyu daga birnin Kermanshah, ranar 8 ga Janairu, sun nuna wasu jami'an tsaro rike da na'uka biyu na bindigogin pistol, wanda kwararru suka ce yana kama da bindiga kirar Beretta 50 ko kuma CZ 75.
Adduna

Asalin hoton, Vahid Online
Masu zanga-zanga da dama su shaida wa BBC cewa an far musu ta hanyar amfani da adduna da kuma wukake. Hotunan da BBC ta samu na gawawwakin wadanda aka kashe sun nuna raunukan adduna da kuma na harbin bindiga.
Hotunan na'urar tsaro ta CCTV daga Tehran suna nuna wani jami'an tsaro na far wa masu zangaz-zangar da ke mafaka a wani gida ta hanyar amfani da adduna.
Haka ma, wani karin bidiyo ranar 8 ga Janairu, ya nuna wani jami'in tsaro na far wa wata 'yar zanga-zanga a kai da adda.
Kulake
Wasu hotunan bidiyo da BBC ta samu sun nuna yadda ake lakada wa mutane duka ta hanyar amfani da kulake.
Lamarin ya kai ga kashe wani mai zanga-zanga, Saghar Seifollahi Fars.











