A birnin Ibadan ake sarrafa sinadarin Akurkura - NDLEA
Hukumar yaki da sha da fatauncin miyagun kwayoyi ta Najeriya ta ce ta gano a cewa a birnin Ibadan na jihar Oyo ake sarrafa sinadarin nan na Akurkura da hukumar ta ce kayan maye ne.
Shugaban hukumar Janar Muhammad Buba Marwa mai ritaya shi ne ya bayyana a haka a wata tattaunawa da BBC a kwanakin baya.
Ya ce a yanzu sun kama mutane da dama da suke amfani da sinadarin, kuma ana fadakar da su kan illar amfani da sinadarin na akurkura.
Ko a karshen makon jiya sai da hukumar ta ce ta kama wani mutum a filin jirgin sama na Kano yana shirin tafiya da su kasar Saudiyya.
Sannan a cikin makon na jiya kuma aka kama wani mutum da kwalbar akurkura fiye da dubu ashirin da shida a Kano din.
A wannan bidiyon, Janar Bubu Marwa mai ritaya ya yi karin bayani kan sinadarin na akuskura.



