Jana'izar Sarauniya Elizabeth ta II: Bankwana na karshe
Jana'izar Sarauniya Elizabeth ta II: Bankwana na karshe
An yi jana'izar Sarauniya Elizabeth II a Cocin Westminster Abbey - ginin da a nan ne aka daura mata aure, kuma aka nada ta a matsayin Sarauniya.
Daruruwan manyan mutane ne suka halarci jana'izarta, ciki har da shugaban Amurka Joe Biden da takwaransa na Faransa Emmanuel Macron, da tsofaffin firaiministoci shida na Birtaniya da ke raye.
An dora akwatin gawarta, wanda aka nade da tutoci da kuma Kambin sarauta, a kan wata igwa da sojojin ruwa suka jagoranta.
Bayan kammala jana'izar, wani jerin gwano ya dauki akwatin gawar Sarauniya a wata tafiyar karshe ta cikin Landan inda suka wuce cincirindon mutane da ke makoki.
Daga can ne kuma gawar ta yi tafiyar karshe zuwa Windsor Castle inda iyalanta suka yi mata jana'izar karshe.



