Tashin farashin dala ne zai sa mu rufe kasuwa - 'Yan canji

Bayanan bidiyo, Latsa wannan alamar bidiyo domin kallo
Tashin farashin dala ne zai sa mu rufe kasuwa - 'Yan canji

Kungiyar 'yan kasuwar canji ta Abuja ta ce daga ranar Alhamis za ta rufe kasuwar canji har sai abin da hali ya yi sakamakon tsadar dala da ake fama da ita a Najeriya.

Shugaban kungiyar, Alhaji Abdullahi Dauran shi ne ya sanar da hakan a wani taron manema labarai a Abuja.