Matashin da ke rayuwar irin ta zamanin kakanninsa

Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon matashin
Matashin da ke rayuwar irin ta zamanin kakanninsa
    • Marubuci, Daga Jamie Russell
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Scotland

Shekarun Callum Grubb 19, amma yana rayuwa irin ta shekarun 1940, wato kimanin shekara 80 da ta wuce.

Kusan duk abin da amfani da su irin na wancan lokacin ne, ciki har da tufafinsa.

Matashin na amfani da wata ƙaramar mota da ka yi yayinta tun shekaraun 1948, da wani keke da aka yi yayinsa a shekarar 1952.

"Na kan tsokani abokina, wannan ya ma zarta ra'ayi,'' in ji shi.

"Ina sha'awar abubuwan tsohon yayi."

.
Bayanan hoto, Callum na sha'awar abubuwa tsoffin yayi irin na 1940
.

Asalin hoton, RON WALKER

Bayanan hoto, Motar Callum ta fi kakarsa da shekara 10

Motar da Callum ke amfani da ita ta fi kakarsa Anne, da shekara 10.

Collum na zaune a gidan kakar tasa da ke unguwar Kirkcaldy, a yankin Fife na ƙasar Scotland, tun yana da shekara 12 a duniya.

A yayin da kakar tasa mai shekara 75 ke amfani da wayar hannu, shi kuwa jikan nata bai taɓa yin waya ba.

"Ni bana sha'awar abu buwan fasaha," in ji Callum.

"An tilasta min mallakar kwamfuta a makaranta, amma na tsane ta."

b
Bayanan hoto, Callum da kakarsa sun shafe shekar bakwai suna zaune a gida ɗaya.

Callum ya ce ya fara soyayya da wata mata mai shekara 40 a lokacin da ya shiga makarantar sakandire.

"Ni ma'abocin son abubuwan tarihi ne," in ji shi.

"A lokacin da ina ƙarami, naka duba littafin adana bayanan yaƙe-yaƙe, kuma abubuwan sukan burgeni sosai."

A yanzu yana da koma da suka danganci wancan lokacin, kamar su fitilar kwai, da kasa-kasan radiyon rikoda da yake sauraron waƙoƙin zamanin da, kamar su Vera Lynn da Anne Shelton da Frank Sinatra.

"Idan ka tambayeni sunan mawaƙi ɗaya a wannna zamani, ba zan iya faɗa maka ba, saboda ban ma san su ba," in ji shi.

.

Wani abu da Collum ya yi fece wajen amfani da shi, shi ne ƙaramar motarsa, ƙirar Austin Cambridge, da ya sanya wa suna Poppy.

Tun yana shekara 13 ya fara tara kuɗi domin sayen motar.

Mahaifiyarsa mai suna Claire ta ce "Callum ya zo ya faɗa min, yana son sayen tsohuwar Austin',"

"Ban taɓa tunanin cewa hakan ba zai faru ba."

Ya sayi motar fam7,000 a farkon Nuwamba daga hannun wani mutum da ya hadu da shi a lokacin da ya ziyarci wani gidan tarihi.

"Ba ta da belet, amma ina matuƙar sonta," in ji Callum.

yana da takardun motar na farko a lokacin da aka saye ta, inda suke nuna cewa an saye ta fam 215 a shekarar 1938, kwatankwacin fama 18,000 a yanzu.

b

Ba haramun ba ne ka tuƙa babbar mota ba tare da ɗaura belet ba, kuma Collum na amfani da motar a kowace rana, tun bayan da ya saye ta.

"Ina jin daɗin tuƙa ta, musamman idan na hau tsoffin titunan ƙasarmu," in ji shi.

"Motar ta taɓa tsallake rijiya da baya daga wani hari da aka taɓa kai mata a Landan,'' in ji shi.

.

Asalin hoton, RON WALKER

Ana yawan ganin Collum a cikin motarsa a unguwar Kirkcaldy, kuma ya zama tamkar wani tauraro a unguwar.

Mafi yawan gidajen biredi kan gayyace shi domin ya faka motarsa a gaban gidajen biredin nasu a lokacin bikin buɗe gidajen.

"Mutane masu shekaru daban-daban na son tsayawa a kusa da motar, yara da manya na sonta,'' in ji Collum.

Yakan yi yawo har zuwa wajen unguwar tare da motar.

"Muna jin daɗin ɗana motar musamman tare da abokaina''.

"Nakan yawaita tsayawa a shagunan sayar da tsoffin kayayyaki domin sayen tsoffin tufafi''.

"Kakata har zaƙuwa take yi na dawo gida, saboda ta san zan dawo da wani abu''.

.

Asalin hoton, RON WALKER

Callum ya ce mutane kan kaɗu idan suka ji labarin cewa bani da waya.

"Kullum mutane so suke yi mu'amala da ni".

Ya shafe lokaci mai tsawo tare da motar tasa, yana kula da ita tare da yi mata gyara, duk da cewa ba a biya mata harajin hanya, kamar sauran motoci da ake ƙera fiye da shekara 40 da suka gabata.

Idan Collum ba ya cikin motarsa, to yana tare da abokansa, ko yana aiki a gidan kiwon karnukansa.

Ya ce yana da abokai masu shekaru daban-daban, sai dai ya fo jin dadin yin abota da mutanen da suka fi shi shekaru sosai.

"Kodayaushe na yi hira da tsofafin mutane, sukan ce min suna tuna iyaye da kakanninsu idan suka ga motata, a lokacin da suka kuma suke da shekaru kamar nawa," in ji shi.

.

Asalin hoton, RON WALKER

Anne Walker, kakar Callum ta ce gidanta ya zama cibiyar ziyara saboda jikan nata.

"Akwai ranar da na tashi da hoton Winston Churchill da tsoffin kasa-kasan rikoda," in ji shi.

Callum ya koma gidan kakarsa tun yana da shekara 12, domin kula da ita bayan rasuwar kakansa .

"Na san abubuwan tarihi masu yawa daga Callum, fiye da yadda na sansu kafin haihuwarsa,' in ji kakar tasa mai shekara 75.

"Mu kan kalli tsoffin fina-finai tare, kuma yana son film din Ginger Rogers," in ji Anne.

b

Mahaifiyar Callum, mai suna Claire, ma'aikaciyar cibiyar kula da renaon yara ce a Fife, ta kuma ce a koyaushe takan ƙarfafa wa ɗan nata gwiwa.

"A makaranta Callum ya koyo wannan ɗabi'a, a lokacin yana da shekara 12,'' in ji ta.

"Abin mamaki ne, na kuma tambaye shi, ina ya koyo wannan al'amari?

"Sai ya ce min haka yake son tufafi na, haka nake son kaina'.

"Tun daga lokacin, Collum ya zama haka'', in ji mahaifiyar tasa.

Claire ta ce abu ne mai kyau Callum yake yi, kuma tana kallonsa a matsayin wanda ya rayu a shekarun 1940.