Bazoum ya musanta zargin tserewa daga Nijar

Asalin hoton, Bazoum
Tawagar lauyoyin da suka yi iƙirarin wakiltar hamɓararren shugaban ƙasar Nijar, Mohamed Bazoum, sun yi watsi da zargin da sojojin mulkin ƙasar suka cewa Bazoum da iyalansa sun yi yunƙurin tserewa daga inda suke tsare.
Cikin wata sanarwa da lauyoyin suka fitar, sun ce Bazoum bai samu ganawa da lauyoyinsa tun bayan kifar da gwamnatinsa.
Haka kuma lauyoyin sun yi watsi da zargin da sojojin mulkin ƙasar suka yi kan tserewar Bazoum, suna masu cewa bai yi wani yunƙuri na tserewa daga ƙasar daga inda ake tsare da shi 'ba bisa ƙa'ida ba'.
Sun ce ya kamata kotu ta tuhumi waɗanda ke tsare da shi.
Tawagar lauyoyin sun kuma ce likitansa ne kawai ke samun damar ganawa da shi, tun bayan tsare shi, to amma shi ma a ranar Juma'a an hana shi ganinsa a ƙoƙarinsa na ai masa abinci.
Iƙirarin sojojin na daƙile yunƙurin Bazoum na tserewa

Asalin hoton, State House
A ranar Alhamis da daddare ne gwamnatin mulkin sojin Nijar ta ce ta daƙile yunƙurin hamɓararren shugaban ƙasar Mohamed Bazoum na tserewa tare da iyalinsa daga inda yake tsare.
Ana tsare da Bazoum da matarsa da kuma ɗansa ne tun bayan da sojoji suka kifar da gwamnatinsa a cikin watan Yuli.
Kakakin gwamnatin sojin Nijar, Kanar-Manjo Amadou Abdramane - wanda ya bayyana hakan cikin jawabin da ya yiwa jama’ar ƙasar ta Talabijin - ya ce Bazoum da iyalinsa sun tsara guduwa daga fadar shugaban ƙasar ne da misalin ƙarfe uku na dare.
Ya ce hamɓararren shugaban ƙasar Mohamed Bazoum ya yi ƙoƙarin tserewa da ƙarfe 3 na daren ranar Alhamis tare da iyalansa da masu dafa masu Abinci biyu da kuma jami’an tsaro guda biyu.
Sai dai a cewar sojojin, wannan yunƙurin da bai kai ga nasara ba ba, na cikin wani tsari da aka shirya da kuma sojojin suka ce suke bi sau da ƙafa.
Kanar-Manjo Amadou Abdramane ya ce ‘’matakin farko na wannan shiri shi ne su fice daga cikin fadar zuwa wani wuri, inda wata mota ke jiransu daga nan ne za a ɗauke su zuwa wani gida da ke cikin unguwar Tchangareya , daga nan kuma a nufi wani wuri inda wasu jirage biyu masu saukar ungulu na wata ƙasa da sanarwar ba ta bayyana ba, za su kai su Birnin Kebbi da ke tarrayar Nijeriya’’
Sanarwar sojojin ta kuma jinjina wa sojojin da hazaƙarsu da kuma hikimarsu ta ba da damar daƙile wannan yunƙurin tare da kare rayuka.
Mohamed Bazoum dai ya kasance tsare tun bayan da jami'an tsaron fadarsa suka kifar da gwamnatinsa suke kuma ci-gaba da yin garkuwa da shi tun ƙarshen watan Yuli.
Bazoum ya ƙi amince da yin murabus
Hamɓararen shugaban ƙasar ya ƙi amincewa ya yi murabus tun bayan da sojojin suka kifar da gamnatinsa, duk kuwa da buƙatar hakan da suka yi daga gare shi.
Lamarin ya yi sanadiyyar raba gari tsakanin ƙasar da uwargijiyarta Faransa ta hanyar ƙorar jakadanta da kuma sojojinta 1500 da ke yaƙi da ƙungiyoyin masu da’awar jihadi a yankin Sahel musaman a yankin iyakoki uku.
Nijar na ɗaya daga cikin ƙawayen ƙasashen yammacin duniya a yankin Sahel da suke yaƙi da ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai, masu alaka da Al-Qaeda da IS.
A kan haka ne ƙungiyoyin yammacin Afrika irin su ECOWAS da UEMOA suka ƙaƙaba wa ƙasar takunkumi domin tilasta wa sojojin mayar da hamɓararren shugaban ƙasar Mohamed Bazoum.
Mohamed Bazoum na da kyakkyawar alaƙa da ƙasashen yamma, musamman Faransa, a yaƙin da suke yi da masu iƙirarin jihadi a yankin Sahel.











