...Daga Bakin Mai Ita tare da Gaye na shirin Dadin Kowa

...Daga Bakin Mai Ita tare da Gaye na shirin Dadin Kowa

Filin Daga Bakin Mai Ita na makon nan, ya tattauna da Abdurrahman Usman, ko kuma Gaye a fitaccen shirin talbijin ɗin Daɗin Kowa na tashar Arewa24.

Jarumin dai wanda aka haifa a garin Dadin Kowa na jihar Filato, ya ce ya yi karatun difloma a fannin kwamfuta, kuma yana da difloma a kan shirye-shiryen fim da na talbijin.

Gaye ya shaida wa BBC cewa a yanzu haka yana karatun digiri a Jami'ar Bayero Kano.