Halin da shirye-shiryen Najeriya ke ciki kan Aikin Hajjin bana
Halin da shirye-shiryen Najeriya ke ciki kan Aikin Hajjin bana
Hukumomin kula da tafiye-tafiyen aikin Hajji a Najeriya sun bayyana kyakkyawan fatan gudanar da aiki mai tsafta, da zai tabbatar duk maniyyacin da ya biya kudinsa ya je Saudiyya don sauke farali a shekarar.
Shugaban riko na hukumar aikin hajji ta kasa, Alhaji Jalal Ahmed Arabi ya shaida wa BBC cewa duk da yake sun bukaci kowanne maniyyaci ya ajiye naira miliyan 4.5 a matsayin kudin kujera, amma suna fatan a karshe maniyyatan bana za su samu rangwame.
Tsadar kudin tafiya aikin hajji zuwa Kasa mai Tsarki na cikin abubuwan da ke ci wa Musulmai tuwo a kwarya, yayin da hukumomi suka fara shirye-shiryen aikin na bana.
Jalal Ahmed Arabi ya ce tsadar kujerar aikin hajjin a yanzu haka, tana barazana ga aniyar cike kujerun da aka ware wa Najeriya.



