Hira da Sani, wani farfesan Amurka da ya fara koyon Hausa a birnin New York

Bayanan bidiyo, Hira da wani Ba'amurke mai sha'awar koyon Hausa
Hira da Sani, wani farfesan Amurka da ya fara koyon Hausa a birnin New York

Farfesa Rudolf Gaudio, wani Ba'amurke ne mai sha'awar koyon harshen Hausa da ya fara koyon harshen a jami'a ya ce al'adun Hausa da suka fi ƙayatar da shi, akwai zaman hira a tsakanin jama'a.

Malamin jami'ar wanda kuma ake kira da suna Sani a ƙasar Hausa, masani ne a fannin nazarin halayya da al'adun al'umma (anthropology).

A wannan bidiyo za ku ji abin da ya yi masa ƙaimi wajen koyon harshen Hausa da nau'o'in abincin da ya fi so da kuma al'adun Hausawa da ya ce sun fi burge shi a rayuwa.